Category: Nigeria
Local Nigerian News
Tsare – Tsaren mu Shi Ya Kawo Saukin Tsananin Rayuwa a Kasar nan – Cardoso
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce gyare-gyaren da ya aiwatar sun taimaka wajen rage tasirin girgizar tattalin arzikin duniya, tare da hana ‘yan Najeriya fuskantar karin tsananin rayuwa. Gwamnan Central Bank of Nigeria, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana haka a yayin taron bazara na World Bank da International Monetary Fund (IMF) da aka gudanar a…
Anchor Borrowers: Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Naira Tiriliyan 1.12
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gina Jiki da Tsaron Abinci ya kaddamar da bincike kan inshorar da aka yi wa shirin Anchor Borrowers na naira tiriliyan 1.12, bayan zarge-zargen karkatar da kudade da ake yi wa ma’aikatu, hukumomi, da cibiyoyin kudi da suka shiga shirin. A zaman sauraron ra’ayi, Manajan Darakta na Nigerian Agricultural Insurance Corporation…
Daukar Nauyin Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya ta Sauya Zargin da ta ke yi wa Malami
Gwamnatin Tarayya ta sauya zarge-zargen da ta ke yi wa tsohon Ministan Shari’ar ƙasar Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdul’aziz inda aka cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci ciki. Gwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiA zaman kotun da aka yi a ranar Laraba, Akinlolu Kahinde wakilin hukumar farin kaya ta Naeriya…
NUJ ta Bukaci Afuwa da Matakin Gwamnati Kan Kalaman Ministan FCT
Kungiyar ‘yan jarida ta Nigeria Union of Journalists (NUJ) ta bayyana matukar kaduwa da fushi kan kalaman da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi kan dan jaridar Channels Television, Seun Okinbaloye. A cikin wata sanarwa, NUJ ta ce furucin Ministan na cewa, “Da akwai yadda zan karya allo, da na harbe shi,” na…
REA Ta Raba Naira Biliyan 9 Domin Ayyukan Mini-Grid
Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara ta Rural Electrification Agency (REA) ta raba kusan Naira biliyan 9 domin tallafawa ayyukan mini-grid a jihohin Taraba, Kogi, Kwara da Neja, a wani bangare na kokarin fadada amfani da makamashin sabuntawa a fadin kasar. A cewar wata sanarwa, an bai wa kamfanin Havenhill Naira biliyan 7.95 domin…
FG Ta Ƙara Tsarin Bashin 2026 Zuwa Naira Tiriliyan 29.2
Gwamnatin Tarayya (FG) ta ƙara adadin bashin da take shirin karɓa a shekarar 2026 zuwa Naira tiriliyan 29.2, bayan da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da ƙarin girman kasafin kuɗi. Wannan sabon adadi ya nuna ƙarin Naira tiriliyan 11.31 idan aka kwatanta da hasashen farko na Naira tiriliyan 17.89 da aka bayyana a cikin…
Bukin Easter: Gwamnatin Tarayya Ta Ayana Juma’a da Litinin Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, da Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutu domin bikin Easter na wannan shekara.Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba. Ya taya Kiristoci a Najeriya da ma na…
Tinubu Ya Nemi Karin Kasafin Kudi na Naira Tiriliyan 9, Jimilla Ta Kai N67.4trn
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta amince da gyaran kasafin kudin shekarar 2026, inda ya nemi karin naira tiriliyan 9 domin daga jimillar kasafin daga N58.4trn zuwa N67.4trn. An isar da bukatar ne ta cikin wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar…
Tinubu Ya Nemi Sabon Rancen Dala Biliyan 6 Daga UAE da Birtaniya
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan karɓar sabbin rance na waje da suka kai dala biliyan 6 domin aiwatar da ayyukan more rayuwa, biyan basussuka, da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa. A cikin wata wasika da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na…
EU Ta Ware Yuro Miliyan 288 Domin Lafiya, Noma da Ci gaban Dijital a Najeriya
Ƙungiyar Tarayyar Turai, European Union, ta sanar da ware yuro miliyan 288 domin tallafawa fannoni daban-daban a Najeriya, ciki har da lafiya, noma, harkokin kudi, hijira, sauyin yanayi da kuma bunƙasa tsarin dijital na gwamnati. An bayyana hakan ne a taron manema labarai na ministoci na EU da Najeriya da aka gudanar a Abuja, wanda…

