Category: Nigeria
Local Nigerian News
Kugiyar Ƙwadago Ta Nemi Haɗa Ma’aikatun Man Fetur da Wutar Lantarki
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafin ₦6 tiriliyan ga kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos), tana mai cewa wannan mataki na wucin gadi ne da ba zai magance matsalar wutar lantarki da ta dade tana addabar ƙasar ba. Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana bangaren…
Eid-el-Fitr: Gwamnatin Tarayya ta Sanar da Alhamin, Jumma’a Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid al-Fitr, wanda ke nuna karshen watan azumin Ramadan.Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya. A wata sanarwa da Sakatare na dindindin a ma’aikatar, Magdalene Ajani,…
Tinubu Ya Nada Tunji Disu Masayin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya kaddamar da Olatunji Disu a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. An gudanar da bikin, wanda ya fara misalin karfe 4:00 na yamma, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara…
Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Ayana Laraba a Matsayin Farkon Azumi
Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ayyana ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Ramadan 1447 Hijiriyya. Sanarwar ta biyo bayan tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi daidai…
Adadin Kuɗaɗen Ajiyar Waje Ya Haura Dala Biliyan 47, Mafi Girma Tun 2018
Ajiyar kuɗaɗen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 47, wanda shi ne mafi girma tun shekarar 2018, alamar ƙarfafa matsayar kuɗin waje ta ƙasar tare da ƙara amincewa da hangen nesa na Babban Bankin Najeriya (CBN). Sabbin bayanai sun nuna cewa ajiyar ya kai dala biliyan 47.025, inda ya zarce rekodin da aka samu…
Najeriya za ta Rage Karɓar Bashi, ta Ƙarfafa Tattara Kuɗaɗen Ciki Gida — Edun
Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziƙi na Ƙasa, Wale Edun, ya ce dole ne Najeriya ta rage dogaro da karɓar bashi tare da ƙarfafa tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, domin daidaita harkokin kuɗi da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa. Edun ya bayyana haka ne a taron horaswa na shugabannin Hukumar Haraji ta…
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Dakatar da Sanata Natasha
Sashen Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, a ranar Litinin, ya tabbatar da matakin da Majalisar Dattawa ta ɗauka na dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta ce majalisar ta yi aiki ne a cikin ikon da doka ta ba ta. A hukunci guda ɗaya da kwamitin alƙalai uku ya yanke a ƙarar da Natasha…
Farfesa Saleh Pakistan Ya Ajiye Aiki a Matsayin Shugaban NAHCON
Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (National Hajj Commission of Nigeria – NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda aka fi sani da Saleh Pakistan, ya ajiye aikinsa daga muƙamin da yake rike da shi. Wata majiya mai tushe ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto,…
Kulla Zuba Jari Nigeriya da Amince da Dala Biliyan 18.2, da Sabbin Filayen Mai 28 — Lokpobiri
Ministan Ƙasa na Albarkatun Man Fetur (Mai), Heineken Lokpobiri, ya bayyana cewa Najeriya ta samu gagarumar nasara a fannin zuba jari a shekarar 2025, bayan kulla sabbin shirye-shiryen bunƙasa filayen mai 28 masu darajar dala biliyan 18.2, tare da hasashen samar da gangar mai biliyan 1.4. Lokpobiri ya bayyana hakan ne a ranar Talata a…
Makamashi: Najeriya Za Ta Haɗa Kai da Afirka, Abokan Hulɗa na Duniya kan Mai Tsabta — Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta yi haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka, abokan hulɗa na duniya da kuma kamfanoni masu zaman kansu domin samar da makamashi mai tsabta, mai araha, mai haɗa kowa da kowa kuma mai ingantaccen tsaro. Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata…

