Trends

Kugiyar Ƙwadago Ta Nemi Haɗa Ma’aikatun Man Fetur da Wutar Lantarki

Kungiyar kwadago na kasa

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafin ₦6 tiriliyan ga kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos), tana mai cewa wannan mataki na wucin gadi ne da ba zai magance matsalar wutar lantarki da ta dade tana addabar ƙasar ba.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana bangaren wutar lantarki a matsayin “babban nauyi mai daure gwiwa” ga ma’aikata da al’umma, yana zargin wasu manyan masu ruwa da tsaki da cin riba ta hanyar bogus din tallafi da karin kudin wuta, yayin da ‘yan Najeriya ke “biyan kudin duhu.”

Ƙungiyar ta ce wannan tallafi alama ce ta matsaloli masu zurfi a tsarin, tare da bukatar gwamnati ta haɗa Ma’aikatar Man Fetur da Ma’aikatar Wutar Lantarki zuwa Ma’aikatar Makamashi guda ɗaya domin tabbatar da gaskiya da kuma fifita samar da wuta a cikin gida.

Bangaren wutar lantarki na Najeriya na fuskantar matsaloli masu tsanani, inda tashoshin samar da wuta 16 cikin 33 suka daina aiki a tsakiyar watan Maris sakamakon katsewar iskar gas saboda bashin da ya haura ₦3 tiriliyan. Hakan ya sa samar da wuta ya ragu zuwa tsakanin megawatt 3,700 zuwa 4,000, ƙasa da ƙarfin da aka girka wanda ya wuce megawatt 13,000.

Ajaero ya soki bangaren man fetur da fifita fitar da kayayyaki da samun kudin waje fiye da samar da iskar gas a cikin gida, lamarin da ya bar Ma’aikatar Wutar Lantarki na fama da faduwar grid da kuma dogaro da dizal da janareto.

NLC ta ce haɗa ma’aikatun zai taimaka wajen tsara harkokin makamashi gaba ɗaya, samar da farashi mai adalci, da kuma tsare-tsaren kudin wuta da suka dace da ingancin sabis, maimakon tsarin “cost-reflective” na yanzu.

Ƙungiyar ta kuma soki sayar da bangaren wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kansu a shekarar 2013, tana mai cewa sun kasa inganta samar da wuta duk da yawan tallafin da suka samu. “Wutar lantarki hidimar jama’a ce kuma hakki ne na asali, ba kayan alatu ba,” in ji ƙungiyar.

A ƙarshe, NLC ta bukaci gwamnati ta dakatar da shirin tallafin, ta kira babban taron masu ruwa da tsaki na ƙasa, tare da samar da wani “taswirar wutar lantarki ta jama’a” da za ta mayar da hankali kan mallakar gwamnati, tsaron makamashi, da jin daɗin ma’aikata da al’umma baki ɗaya.