Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta yi haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka, abokan hulɗa na duniya da kuma kamfanoni masu zaman kansu domin samar da makamashi mai tsabta, mai araha, mai haɗa kowa da kowa kuma mai ingantaccen tsaro.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe taron Nigeria International Energy Summit na 9, wanda aka gudanar a Dakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa (State House Banquet Hall), Abuja. Taron ya samu halartar shugabannin tawaga da manyan jami’an gwamnatoci daga sassa daban-daban na duniya, shugabannin ƙungiyoyin makamashi na ƙasa da ƙasa, manyan daraktocin kamfanonin makamashi na gida da na waje, cibiyoyin samar da kuɗin bunƙasa, da wakilan al’ummomin da ayyukan makamashi ke gudana a cikinsu.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce makamashi na taka muhimmiyar rawa a zaman lafiyar duniya, bunƙasar tattalin arziki da daidaiton ƙasashe. Ya ƙara da cewa Najeriya ta mayar da hankali sosai kan amfani da dimbin iskar gas a matsayin makamashin sauyi, tare da faɗaɗa makamashin sabuntawa (renewable energy).
“Dole ne makamashi ya haɗa al’umma, ya daidaita tattalin arziki, ya kuma tabbatar da makoma. Dole ne ya ba masana’antu ƙarfi, ya haskaka gidaje, ya tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙire, tare da gina amincewa tsakanin gwamnati, masu zuba jari da al’umma. Najeriya a shirye take ta haɗa kai da Afirka, abokan hulɗa na duniya da kamfanoni masu zaman kansu domin samar da makamashi mai tsaro, mai araha, mai tsabta kuma mai haɗa kowa,” in ji shi.
Shugaban ƙasar ya tuna cewa duk da yalwar damar da sashen makamashi ke da ita a 2023, gwamnatinsa ta gada sashen cikin tangarda sakamakon rashin inganci, rashin tabbas da kuma ƙarancin zuba jari na dogon lokaci.
“Mun fara aiki ba tare da hayaniya ba, da fahimtar cewa ba za a ɗauki makamashi a matsayin kaya na kasuwanci kawai ba idan ana neman zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji Tinubu, yana mai jaddada cewa makamashi ginshiƙi ne na tsaron ƙasa, bunƙasar masana’antu, haɗin kan al’umma da haɗin gwiwar yankuna.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar gina tsarin makamashi mai inganci, gaskiya, dorewa da riba ga kowa.
Dangane da matakan da gwamnatinsa ke ɗauka, Tinubu ya ce an ci gaba da cikakken aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur (Petroleum Industry Act – PIA), tare da ƙarfafa hukumomin sa ido domin fayyace ayyuka, tabbatar da gaskiya da ƙara amincewar masu zuba jari.
Ya ce a ƙarƙashin gwamnatinsa, ayyukan upstream sun samu gagarumar farfaɗowa, inda adadin rigs ya tashi daga takwas a 2021 zuwa 69 a ƙarshen 2025, alamar ƙaruwa a bincike da hako mai.
Tinubu ya ƙara da cewa an cimma manyan yarjejeniyoyin zuba jari (Final Investment Decisions) da suka haura dala biliyan 8, ciki har da manyan ayyukan iskar gas a teku, tare da dawowar zuba jari daga ƙasashen waje sakamakon tabbacin doka, gyaran haraji da ingantaccen yanayin aiki.
Ya kuma bayyana cewa satar danyen mai, wadda ta dade tana rage samarwa da kudaden shiga, ta ragu matuƙa sakamakon ƙarfafa tsaro, sa ido da aiwatar da doka, lamarin da ya dawo da kwanciyar hankali da amincewa da samarwar Najeriya a kasuwannin duniya.
A nasa jawabin, Shugaban ƙasar Gambiya, Adama Barrow, ya ce manufofin Najeriya na da tasiri mai faɗi fiye da iyakokinta, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwa ta dabaru ita ce mabuɗin warware matsalolin yankin da tabbatar da tsaron makamashi.
Shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya ce dole ne Afirka ta daina zama mai fitar da albarkatun ƙasa kawai, ta maida hankali kan sarrafa su domin amfanin al’ummomi da tsara makomar ’ya’ya masu zuwa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a jawabin da aka karanta a madadinsa, ya ce a Afirka, batun makamashi ba wai albarkatu kaɗai ba ne, illa ci gaba mai dorewa da haɗa kowa da kowa. Ya tabbatar da cewa Majalisar Tarayya a shirye take ta bayar da goyon bayan doka ga duk wani yunƙuri da zai tabbatar da cewa idan tsarin makamashi ya yi aiki yadda ya kamata, tattalin arziki zai ƙara ƙarfi da juriya.
