Trends

Ci Gaban GDP na Najeriya Zai Zarce na Aljeriya a 2026 — IMF

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF)

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ce ana sa ran Najeriya za ta sake kwato matsayinta na tattalin arziki na uku mafi girma a Afirka a shekarar 2026.

Bisa bayanan World Economic Outlook na IMF (fitowar Oktoba 2025), Najeriya ta kasance ta huɗu a shekarar 2025, inda GDP ɗinta ya kai kusan dala biliyan 285. A wancan lokaci, Afirka ta Kudu ce ta jagoranta da dala biliyan 426, sai Masar da dala biliyan 349, yayin da Aljeriya ta rike matsayi na uku da dala biliyan 288.

Sai dai hasashen IMF ya nuna cewa GDP na Najeriya zai tashi zuwa kusan dala biliyan 334 a 2026, wanda zai zarce na Aljeriya da ake sa ran zai kai dala biliyan 284. Wannan sauyi zai sanya Najeriya a bayan Afirka ta Kudu (dala biliyan 443) da Masar (dala biliyan 399) kaɗai a jerin tattalin arzikin Afirka.

IMF ta danganta wannan ci gaba da ƙaruwa a samar da danyen mai, ingantuwar samun kuɗaɗen waje (foreign exchange), da kuma tasirin gyare-gyaren tattalin arziki da ake aiwatarwa, ciki har da cire tallafin man fetur, ’yantar da farashin musayar kuɗi, da sake fasalin harkokin kuɗaɗen gwamnati.

Ko da yake waɗannan manufofi sun haifar da matsin hauhawar farashi na ɗan lokaci, IMF ta ce ana sa ran za su ƙarfafa ci gaban tattalin arziki a matsakaicin lokaci.

Matsayin tattalin arzikin Najeriya ya taɓa sauyawa a ’yan shekarun nan sakamakon rage darajar kuɗi, sake lissafin GDP (rebasing), da kuma manyan ƙalubalen tattalin arziki da ke fuskantar ƙasashen Afirka.

Duk da haka, ana samun ƙwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin ƙasar, inda IMF da Bankin Duniya suka ɗaga hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya na 2026 zuwa kashi 4.4%, alamar amincewa da farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar.