Trends

NUJ ta Bukaci Afuwa da Matakin Gwamnati Kan Kalaman Ministan FCT

Kungiyar ‘yan jarida ta Nigeria Union of Journalists (NUJ) ta bayyana matukar kaduwa da fushi kan kalaman da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi kan dan jaridar Channels Television, Seun Okinbaloye.

A cikin wata sanarwa, NUJ ta ce furucin Ministan na cewa, “Da akwai yadda zan karya allo, da na harbe shi,” na nuna barazana kai tsaye da kuma kokarin tsoratar da ‘yan jarida, lamarin da ke barazana ga ‘yancin aikin jarida da ginshikin dimokuradiyya a Najeriya.

Kungiyar ta ce ta jinkirta fitar da wannan sanarwa ne da fatan cewa Ministan zai sake nazari ya kuma janye kalamansa tare da bayar da hakuri cikin gaggawa, amma rashin yin hakan ya kara nuna cewa kalaman ba kuskure na lokaci guda ba ne, illa wata manufa ta tsoratarwa.

NUJ ta bayyana cewa wannan shiru daga bangaren Ministan ya kara tayar da hankali, yana kuma karfafa zargin cewa an yi kalaman ne da gangan domin tsoratar da kafafen yada labarai.

Kungiyar ta kara da cewa irin wadannan kalamai daga babban jami’in gwamnati na haifar da yanayin tsoro ga ‘yan jarida da ke kokarin gudanar da aikinsu cikin gaskiya, tare da aika sakon cewa rahotannin gaskiya na iya jawo barazana ko tashin hankali.

Don haka, NUJ ta bukaci Ministan da ya bayar da hakuri ba tare da sharadi ba kan kalaman da ta kira abin takaici.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta fito fili ta yi Allah wadai da wannan barazana, tare da daukar matakai na kare ‘yan jarida da tabbatar da ‘yancin kafafen yada labarai.

Kungiyar ta kuma yi kira ga dukkan kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula, da masu rajin dimokuradiyya da su hada kai domin kare ‘yancin fadin albarkacin baki.

Shugaban kasa na NUJ, Alhassan Yahya Abdullahi, ya jaddada cewa tsaron ‘yan jarida yana da matukar muhimmanci ga ingantacciyar dimokuradiyya, yana mai cewa duk wani yunkuri na danne muradunsu dole ne a tunkare shi da hadin kai da tsayin daka.