Trends

FG Ta Ƙara Tsarin Bashin 2026 Zuwa Naira Tiriliyan 29.2

Gwamnatin Tarayya (FG) ta ƙara adadin bashin da take shirin karɓa a shekarar 2026 zuwa Naira tiriliyan 29.2, bayan da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da ƙarin girman kasafin kuɗi.

Wannan sabon adadi ya nuna ƙarin Naira tiriliyan 11.31 idan aka kwatanta da hasashen farko na Naira tiriliyan 17.89 da aka bayyana a cikin takardar shirin kasafin kuɗin 2026.

Sabon tsarin ya fito ne a cikin Dokar Kasafin Kuɗi da takardar zaman Majalisar Wakilai mai kwanan wata 31 ga Maris, 2026.

Jimillar kashe kuɗi yanzu ta kai Naira tiriliyan 68.32, yayin da ake hasashen samun kudaden shiga na Naira tiriliyan 36.87, wanda hakan ya bar gibin kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 31.46.

Ana sa ran za a cike mafi yawan wannan gibi ne ta hanyar karɓar bashi, yayin da sayar da kadarorin gwamnati da shirin keɓance wasu kamfanoni zai samar da kusan Naira biliyan 189 kacal, sai kuma bashin da aka ɗaura wa ayyuka wanda zai kai kusan Naira tiriliyan 2.05.

Biyan bashin da ake da shi kaɗai zai lakume Naira tiriliyan 15.81, inda Naira tiriliyan 10.16 za su tafi kan bashin cikin gida, yayin da Naira tiriliyan 5.36 za su tafi kan bashin ƙasashen waje, abin da ke nuna yadda nauyin bashi ke ƙaruwa a ƙasar.

Kasafin kuɗin da ba na biyan bashi ba (recurrent) ya kai Naira tiriliyan 15.43, yayin da aka ware Naira tiriliyan 32.29 domin ayyukan raya ƙasa (capital projects).

‘Yan majalisa sun bayyana cewa ƙarin kasafin an yi shi ne domin biyan tsofaffin basussuka, samar da kuɗaɗen gina ababen more rayuwa, ƙarfafa bangaren shari’a, bunƙasa harkar lafiya, da kuma shirye-shiryen zaɓen 2027.

Haka kuma, sun ƙara farashin danyen mai a kasafin da dala 10 kan kowace ganga, wanda ake sa ran zai samar da Naira tiriliyan 2.59, tare da ƙarin kudaden haraji daga kamfanonin sadarwa, ciki har da Naira biliyan 724 daga MTN da Naira biliyan 150 daga Airtel.

Duk da waɗannan matakai, an ƙara bashin waje da Naira tiriliyan 6.16, yayin da Majalisar Dattawa ta riga ta amince da bukatar sabon bashin dala biliyan 6 da Shugaban Ƙasa ya gabatar.

Masu sukar wannan mataki, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, sun yi gargadin cewa “karɓar bashi ba tare da ƙa’ida ba, tare da amincewar majalisa ba tare da cikakken nazari ba, na da haɗari,” yana mai cewa makomar Najeriya “ba za a iya sayar da ita cikin gaggawa ba.”

Masana tattalin arziki kamar su Dakta Muda Yusuf da Dakta Aliyu Ilias sun yi gargaɗi cewa yawaitar gibin kasafin na iya haifar da hauhawar farashi, raunana tattalin arziki, da kuma jefa ƙasar cikin tarkon bashi.

“Ya kamata mu damu da dorewar bashi… yawan gibin kasafi na iya takaita damar gudanar da harkokin gwamnati,” in ji Yusuf.

Kungiyoyin farar hula ma sun nuna damuwa cewa bashin da ake karɓa bai haifar da ci gaba ba. Joseph Amenaghawon na BudgIT ya ce, “Abin da ake samu shi ne bashi ba tare da ci gaba ba. An aro kuɗi amma ba a saka su yadda ya kamata ba.”

Ya bukaci a sanya ido sosai domin tabbatar da cewa basussukan da ake karɓa suna tallafawa manyan ayyukan da za su kawo ci gaba, ba wai kashe su a kan al’amuran yau da kullum ba.