Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da shirin biyan bashin da ake bin ɓangaren wutar lantarki domin kawo ƙarshen tsofaffin basussuka a ƙarƙashin shirin gyaran harkokin wutar lantarki na ƙasa.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta ce an cimma matsayar biyan bashin ne bayan kammala duba dukkan tsofaffin basussukan da suka addabi ɓangaren wutar lantarki fiye da shekara goma.
An bayyana cewa basussukan sun taru ne tsakanin watan Fabrairun 2015 zuwa Maris 2025. Bayan tantancewa, an amince da biyan jimillar naira tiriliyan 3.3 a matsayin cikakken sulhu na ƙarshe, domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen warware matsalar.
A cewar sanarwar, an fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wutar lantarki 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kuɗi da ya kai naira tiriliyan 2.3. Gwamnatin tarayya ta riga ta tara naira biliyan 501 domin fara biyan bashin, inda aka riga aka fitar da naira biliyan 223, yayin da ake ci gaba da sauran biyayya.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen inganta samar da wutar lantarki a ƙasa.
“Ma’anar hakan ga ‘yan Najeriya ita ce, da zarar kuɗi ya fara shiga sassan samar da wutar lantarki, za a samu kwanciyar hankali a samarwa. Taimakawa kamfanonin wuta zai inganta samun lantarki mai dorewa,” in ji sanarwar.
Ta kuma ƙara da cewa, yayin da ɓangaren ke daidaituwa, za a samu karin zuba jari, karin ayyukan yi, da ingantaccen sabis ga jama’a.
Mashawarciya ta musamman kan harkokin makamashi ga shugaban ƙasa, Olu Arowolo-Verheijen, ta ce shirin ba wai kawai biyan tsofaffin basussuka ba ne, har ma da dawo da amincewa a dukkan sassan wutar lantarki.
“Za a tabbatar masu samar da gas sun samu kuɗinsu, kamfanonin wuta za su ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma tsarin zai fara inganta,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa wannan na daga cikin manyan sauye-sauye da ake aiwatarwa, ciki har da inganta tsarin mitoci da kuma tsarin farashin sabis wanda ke haɗa abin da ake biya da ingancin wutar da ake samu.
Gwamnati ta kuma ce tana bai wa kamfanoni, masana’antu da ƙananan sana’o’i fifiko wajen samar da wutar lantarki, domin wutar lantarki mai inganci na da matuƙar muhimmanci ga samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yabawa dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen warware matsalolin da suka dade suna addabar ɓangaren wutar lantarki, tare da tabbatar da cewa za a fara mataki na gaba na shirin (Series II) a cikin wannan zangon.
