Trends

EU Ta Ware Yuro Miliyan 288 Domin Lafiya, Noma da Ci gaban Dijital a Najeriya

Ƙungiyar Tarayyar Turai, European Union, ta sanar da ware yuro miliyan 288 domin tallafawa fannoni daban-daban a Najeriya, ciki har da lafiya, noma, harkokin kudi, hijira, sauyin yanayi da kuma bunƙasa tsarin dijital na gwamnati.

An bayyana hakan ne a taron manema labarai na ministoci na EU da Najeriya da aka gudanar a Abuja, wanda ya jaddada sabon ƙudurin haɗin gwiwa a ƙarƙashin shirin EU-Nigeria Partnership.

Da yake jawabi a wajen taron, Darakta Janar na Harkokin Haɗin Gwiwar Ƙasashen Waje na Hukumar Tarayyar Turai, Stefano Signore, ya ce tallafin na nuna ƙara zuba jari da EU ke yi wajen bunƙasa Najeriya.

Ya bayyana cewa fannoni kamar lafiya da noma na daga cikin manyan abubuwan da aka fi mayar da hankali a kai, musamman wajen inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida da kuma tabbatar da haɗin kai ga kowa.

Shirin ya yi dai-dai da manufar Global Gateway Strategy, wadda ke da nufin hanzarta zuba jari da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin EU da Najeriya.

Signore ya ƙara da cewa EU na kuma ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin hijira, tare da samar da ingantattun damammaki ga ‘yan Najeriya da ke dawowa gida.

Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Najeriya, Abubakar Bagudu, ya maraba da wannan ci gaba, yana mai cewa wani ɓangare ne na ci gaba daga tattaunawar dabaru ta 2023 tsakanin EU da Najeriya.

Ya ce, “Haɗin gwiwarmu na ƙara karkata zuwa tsarin zuba jari mai haifar da sakamako da kuma tasiri, wanda ya dace da burinmu da sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.”

Bagudu ya jaddada cewa a ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, Najeriya na aiwatar da muhimman gyare-gyaren tattalin arziki domin daidaita yanayin tattalin arziki da samar da damar ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.

Daga cikin yuro miliyan 288 da aka ware, yuro miliyan 50 za su tallafa wa masana’antar kayan lafiya ta hanyar Bank of Industry, yayin da yuro miliyan 85 za su shiga sarkar darajar kasuwancin noma kamar madara da koko. Haka kuma, yuro miliyan 108 za a raba su tsakanin tallafi da rance ga gwamnatin Najeriya.

Sauran kudaden sun haɗa da yuro miliyan 23 don bunƙasa tsarin dijital na gwamnati, yuro miliyan 5 don horo a fannin lafiya da abinci mai gina jiki, yuro miliyan 16 don tafiyar da harkokin hijira, da yuro miliyan 1 don haɗin gwiwar noma da sauyin yanayi.

Manajan Darakta na Bankin Masana’antu, Olasupo Olusi, ya ce wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samar da dogon lokaci na jari a fannoni masu muhimmanci.

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwa da European Investment Bank zai ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida tare da tallafa wa juriyar tattalin arzikin ƙasa.

Haka kuma, Mataimakin Sakataren Harkokin Kasuwancin Waje na Finland, Jarno Syrjaia, ya sanar da cewa ƙasarsa za ta jagoranci ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan dijital na gwamnati a Najeriya ƙarƙashin shirin Team Europe Initiative, ciki har da tallafawa shirin Three Million Technical Talents.

Tarayyar Turai na ci gaba da ƙara zuba jari a Najeriya a matsayin ɓangare na babban shirin zuba jari na yuro biliyan 150 a Afirka, inda Najeriya ke daga cikin manyan ƙasashen da ke amfana.

A bara ma, EU ta ware yuro miliyan 300 domin ayyuka a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na Najeriya, musamman a yankunan da ke fama da rashin tsaro da ƙarancin ci gaba.