Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gina Jiki da Tsaron Abinci ya kaddamar da bincike kan inshorar da aka yi wa shirin Anchor Borrowers na naira tiriliyan 1.12, bayan zarge-zargen karkatar da kudade da ake yi wa ma’aikatu, hukumomi, da cibiyoyin kudi da suka shiga shirin.
A zaman sauraron ra’ayi, Manajan Darakta na Nigerian Agricultural Insurance Corporation (NAIC), Dayo Babaronti, ya bayyana cewa kamfanin ya samar da inshora ta naira biliyan 109 kacal ga manoma 207,514 da ke cikin shirin.
Ya bayyana cewa duk da cewa an fara nada NAIC a matsayin kamfanin inshora daya tilo, daga baya Central Bank of Nigeria (CBN) ya bai wa kamfanonin Veritas Kapital Insurance da Leadway Insurance kwangilar shiga cikin shirin. Sai dai babu daya daga cikin kamfanonin da ya aika wakili zuwa zaman sauraron.
Babaronti ya kara da cewa inshorar da NAIC ta bayar ya kai kashi 12 cikin 100 ne kacal na daukacin shirin, yayin da a cikin shirin bayar da rancen noma na naira biliyan 250 na NIRSAL Plc, NAIC ta bayar da inshora ta naira biliyan 8.25 kacal.
Haka kuma ya bayyana cewa NAIC ta inshora gonakin citta da darajarsu ta kai naira miliyan 715 ne kawai daga cikin naira biliyan 1.6 da aka ware wa shirin, yayin da wasu shirye-shirye kamar na Bankin Masana’antu na sarrafa abinci da noma suka bar NAIC gaba daya.
Shugaban kwamitin, Okafor, ya ce binciken farko ya nuna cewa ba a hada manoma da kungiyoyin kayayyakin noma wajen tsara wadannan tsare-tsare ba, lamarin da ya taimaka wajen rashin nasarar su yadda ake fata.
“Dalilin da ya sa muke nan shi ne saboda shirye-shiryen ba su yi nasara dari bisa dari ba. Da sun yi, da ba za mu zo nan ba,” in ji shi.
‘Yan majalisar sun yi alkawarin gano dukkan matsalolin da suka hana nasarar shirye-shiryen gwamnati na bunkasa samar da abinci, suna mai jaddada cewa gaskiya da rikon amana a fannin inshora na da matukar muhimmanci.
Ana sa ran binciken zai fayyace yadda aka rarraba kudade, dalilan karancin inshora, da kuma ko shirin ya cimma burinsa na bunkasa fannin noma a Najeriya.


