Najeriya ta fitar da gangar danyen mai miliyan 55.39 a cikin watanni biyu na farkon shekarar 2026, duk da cewa matatar mai ta Dangote na fama da karancin danyen mai daga cikin gida.
Bayanan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar sun nuna cewa an fitar da gangar mai miliyan 31.31 a watan Janairu da kuma miliyan 24.08 a watan Fabrairu, inda kusan gangar miliyan 26.55 kacal suka rage domin matatun cikin gida.
Duk da cewa Najeriya ita ce kasa mafi yawan samar da mai a Afirka, matatar Dangote mai karfin tace gangar mai 650,000 a rana ta dade tana korafin cewa ba ta samun isasshen danyen mai daga cikin gida, lamarin da ke tilasta mata shigo da mai daga kasashen waje.
Daga watan Oktoba na 2025 zuwa tsakiyar watan Maris na 2026, matatar ta fuskanci gibin gangar mai kusan miliyan 79.53, inda ta samu gangar miliyan 29.21 kacal daga cikin bukatar miliyan 108.74. Wannan na nufin ta samu kashi 26.9 cikin 100 ne kawai na abin da take bukata.
Dangote ta bayyana cewa tana bukatar gangar mai miliyan 19.77 a kowane wata, amma abin da aka rika kawo mata ya yi kasa sosai—miliyan 4.55 a Oktoba, 6.45 a Nuwamba, 4.30 a Disamba, 5.65 a Janairu, da 4.66 a Fabrairu. A watan Maris kuma, an kawo gangar miliyan 3.6 ne kacal a rabin farko na watan.
Matatar ta zargi masu hakar mai na cikin gida da kin bin dokar samar da mai kamar yadda Dokar Masana’antar Man Fetur ta tanada, yayin da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya tabbatar da cewa yana sayo danyen mai daga wasu kamfanoni a farashin kasuwar duniya domin tallafa wa aikin matatar.
Farashin fetur ya haura naira 1,300 kan kowace lita a lokacin rikicin Iran da Amurka, kafin daga bisani ya sauka zuwa naira 1,250. Dangote ta kare karin farashin, tana danganta shi da tsadar shigo da danyen mai daga waje.
Masu ruwa da tsaki a masana’antar, ciki har da kungiyar masu matatar mai ta Najeriya, sun bukaci a kara samar da danyen mai ga matatun cikin gida, suna mai jaddada cewa samun wadataccen mai akai-akai na da muhimmanci wajen tabbatar da riba da kuma tsaron makamashi a kasar.



