Anchor Borrowers: Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Naira Tiriliyan 1.12
Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gina Jiki da Tsaron Abinci ya kaddamar da bincike kan inshorar da aka yi wa shirin Anchor Borrowers na naira tiriliyan 1.12, bayan zarge-zargen karkatar da kudade da ake yi wa ma’aikatu, hukumomi, da cibiyoyin kudi da suka shiga shirin. A zaman sauraron ra’ayi, Manajan Darakta na Nigerian Agricultural Insurance Corporation…



