Category: Business
Business
Ribar Lamuni: Kashi 63% na ‘Yan Najeriya Sun Nemi A Rage Yawan — CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa kashi 63.3 cikin 100 na ‘yan Najeriya na son a rage yawan ribar lamuni (interest rate), a cewar rahoton bincikensa na hasashen hauhawar farashi na watan Afrilu 2026, gabanin taron kwamitin kula da manufofin kudi (MPC) da aka shirya yi a ranakun 19–20 ga Mayu. Rahoton, wanda sashen…
Rikici a Gabas Ta Tsakiya: Danyen Mai ya Tashi Zuwa $109.3 Yayin DaKara Tsananta
Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya tashi zuwa dala $109.3 kan kowace ganga a ranar Lahadi, sakamakon karuwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda bayanai daga Oilprice.com suka nuna. Wannan tashin farashi ya biyo bayan gargadin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ga Iran, inda ya ce “lokaci na kurewa”…
Masu Sayar da Man Fetur Sun Yi Fatali da Karar Dangote Kan Shigo da Fetur
Sabuwar takaddama ta barke a bangaren kasuwancin mai a Najeriya, inda dillalan mai da masu ajiye fetur suka yi watsi da karar da matatar Dangote Petroleum Refinery ta shigar kotu kan batun hana shigo da fetur daga kasashen waje. Matatar ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Legas tana neman a soke lasisin shigo da…
Kananan Masana’antu: BOI Ta Samu Tallafin Dala Miliyan 200 daga AfDB
Bankin Masana’antu na Najeriya, Bank of Industry, ya samu tallafin lamuni na dala miliyan 200 daga African Development Bank domin fadada samar da dogon zangon jari ga kamfanonin Najeriya da ke muhimman bangarorin tattalin arziki. A cewar AfDB, za a yi amfani da kudaden wajen tallafa wa bangarorin ababen more rayuwa, sufuri, sarrafa kayan abinci…
‘Yan Najeriya Sun Kashe Tiriliyan ₦5.43 Kan Fetur a Watanni Uku na Farkon 2026
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya sun kashe akalla tiriliyan ₦5.43 wajen sayen man fetur (PMS) a watanni ukun farko na shekarar 2026. Binciken da aka yi kan alkaluman Hukumar Kula da Masana’antar Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa an amfani da lita biliyan 4.88 na fetur…
Dangote Zai Kara Zuba Jari zuwa Dala Biliyan 4 a Habasha
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da shirin kara yawan jarin da kamfaninsa ke zubawa a kasar Habasha daga dala biliyan 2.5 zuwa sama da dala biliyan 4, domin karfafa masana’antu da samar da wadataccen abinci a Afirka. Dangote ya bayyana hakan ne a garin Gode da ke yankin Somali na Habasha yayin…
Kin Ƙarin Hannun Jari: IPMAN Ta Bukaci NNPC Ta Farfaɗo da Matatun Mai
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Masu Kasuwar Man Fetur Mai Zaman Kansu ta Najeriya, Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria, Chinedu Ukadike, ya soki Nigerian National Petroleum Company Limited kan yunƙurinta na ƙara hannun jari a Dangote Petroleum Refinery duk da halin da matatun man gwamnati ke ciki. Ukadike ya yi wannan martani ne bayan…
Najeriya Za Ta Jawo Zuba Jarin Waje Dala Biliyan 20 a 2026 – Tinubu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya na kan hanyar jawo kusan dala biliyan 20 na jarin waje kai tsaye (FDI) a shekarar 2026 kaɗai. Tinubu ya danganta hakan da cire matsalolin da suka daɗe suna hana zuba jari, daidaita tattalin arziki da kuma gyare-gyaren da gwamnatinsa ta yi domin ƙara gaskiya da…
Mashigin Hormuz: Farashin Mai Ya Sauka Yayin da Jiragen Ruwa Suka Fara Wucewa
Duk da cewa har yanzu ƙasashen United States da Iran ba su cimma matsaya kan sake buɗe mashigin ruwa na Hormuz ba, rahotanni sun nuna cewa kusan jiragen ruwa 30 na ƙasar China sun ratsa mashigin a ranar Laraba. Kamfanin dillancin labarai na Fars da ke da alaƙa da gwamnatin Iran ya ruwaito cewa tun…
Dangote Ya Ƙi Ƙarin Hannun Jarin NNPC a Matatar Mai
Shugaban rukunin kamfanonin Aliko Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa ya ƙi amincewa da yunƙurin da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, Nigerian National Petroleum Company Limited, ya yi na ƙara hannun jarinsa a Matatar Man Fetur ta Dangote. Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shugaban Asusun Arzikin Ƙasar Norway, Nicolai Tangen….

