Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa kashi 63.3 cikin 100 na ‘yan Najeriya na son a rage yawan ribar lamuni (interest rate), a cewar rahoton bincikensa na hasashen hauhawar farashi na watan Afrilu 2026, gabanin taron kwamitin kula da manufofin kudi (MPC) da aka shirya yi a ranakun 19–20 ga Mayu.
Rahoton, wanda sashen kididdiga na Central Bank of Nigeria ya fitar, ya nuna cewa kashi 26% na mutane na son a bar ribar yadda take, yayin da kashi 10.7% ke goyon bayan a kara ta, duk da matsin lambar hauhawar farashi a kasar.
Binciken ya kuma nuna cewa akwai karuwar fahimta da amincewa da bayanan bankin, inda kashi 92.1% ke nuna cewa suna bin bayanan CBN, yayin da kashi 93.3% ke ganin bankin na da gaskiya da bayyana bayanai cikin kwarewa.
Sai dai rahoton ya nuna cewa hauhawar farashi na kara tabarbarewa, inda kashi 67.2% na mutane suka ce farashin kayayyaki ya yi yawa a watan Afrilu, idan aka kwatanta da kashi 56.4% a watan Maris.
Rahoton ya kuma nuna cewa gidaje (households) sun fi fuskantar matsin lamba fiye da kamfanoni, inda kashi 68.8% na gidaje suka ce farashi ya yi tsada, yayin da kashi 65.9% na kamfanoni suka yi irin wannan korafi.
Kamfanonin kanana (micro businesses) ne suka fi nuna damuwa da hauhawar farashi da kashi 69.9%, yayin da kamfanonin matsakaici suka fi kankanta da kashi 63.2%.
Binciken ya kuma nuna bambancin matakan kudin shiga: gidajen da ke samun kasa da ₦70,000 a wata sun fi jin tsadar rayuwa sosai da kashi 77.9%, yayin da wadanda ke samun ₦250,001 zuwa ₦350,000 suka fi kankanta da kashi 46.6%.
A yankunan karkara kuwa, kashi 70.4% na mutane sun ce suna jin tsadar rayuwa sosai, idan aka kwatanta da kashi 67.6% a birane.
Masu amsa tambayoyin sun bayyana cewa tsadar makamashi, sufuri, matsalar darajar musayar kudi, rashin tsaro da matsalolin ababen more rayuwa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi.
Duk da haka, wasu sun nuna fata cewa matsin lambar farashi na iya raguwa cikin watanni shida masu zuwa.
Masanin tattalin arziki, Muda Yusuf, ya yi gargadin cewa karin tsaurara manufofin kudi na iya cutar da bunkasar tattalin arziki, yana mai cewa tattalin arzikin Najeriya na da rauni kuma yana fuskantar matsalolin tsari.
Ya ce karin tsaurarawa na iya rage samar da lamuni, rage jarin kasuwanci da kuma dakile farfadowar tattalin arziki, inda ya bukaci a yi tsarin da ya dace tsakanin tsaurarawa da sassautawa.
Masu sharhi a United Capital Plc sun yi hasashen cewa MPC zai ci gaba da barin ribar lamuni a matakin 26.5%, tare da barin CRR a 45% da kuma liquidity ratio a 30%, suna masu cewa hauhawar farashi a yanzu ya fi danganta da matsalolin samar da kayayyaki fiye da tsadar lamuni.
