Shugaban rukunin kamfanonin Aliko Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa ya ƙi amincewa da yunƙurin da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, Nigerian National Petroleum Company Limited, ya yi na ƙara hannun jarinsa a Matatar Man Fetur ta Dangote.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shugaban Asusun Arzikin Ƙasar Norway, Nicolai Tangen. Ya ce dalilin ƙin amincewar shi ne shirin da ake yi na fitar da matatar zuwa kasuwar hannayen jari domin bai wa ’yan Najeriya damar mallakar kaso a cikinta.
Tun a shekarar 2021 ne NNPC ta sayi kaso 7.25 cikin ɗari na matatar kan dala biliyan ɗaya, tare da damar ƙara wani kaso na 12.75 cikin ɗari kafin watan Yunin 2024. Sai dai kamfanin bai cika wannan yarjejeniya ba. Dangote ya ce daga baya NNPC ta sake neman ƙarin hannun jari, amma kamfaninsa ya ƙi amincewa.
Ya bayyana cewa rashin daidaiton manufofi daga gwamnati na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar harkokinsa, baya ga rikice-rikicen cikin gida. A cewarsa, “Mu ne muka ce a’a, domin muna son mu bai wa kowa damar zama wani ɓangare na wannan aiki.”
Sabbin bayanai sun nuna cewa matatar Dangote ta samar da lita biliyan 3.18 na fetur a zangon farko na shekarar 2026, wanda kuɗinsa ya haura naira tiriliyan 3.2. A lokaci guda kuma, shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ragu sosai zuwa lita miliyan 965.52 kacal. Matsakaicin farashin fetur daga matatar ya kai kusan naira 1,000 kan kowace lita.
Dangote ya kuma bayyana cewa masu hannun jari a kamfanoninsa da suka haɗa da siminti, takin zamani da sinadarai za su rika karɓar ribar hannun jari ne a dala, saboda kusan kashi 80 cikin ɗari na kuɗaɗen shiga na fitowa daga kasuwannin ƙetare.
Ya tuna yadda ya sayar da kadarorinsa da ke Amurka da Birtaniya domin mayar da hankali gaba ɗaya kan Najeriya. Ya ce, “Ina son zama a Najeriya domin mayar da hankali sosai. Dukkan kasuwancina suna da manufa, kuma mun tsara hangen nesa zuwa shekarar 2030 tare da burin da ya kamata mu cimma.”
Bayanan masana’antu sun nuna cewa matatun cikin gida na ƙara taka muhimmiyar rawa wajen samar da fetur a Najeriya, inda suka rufe kashi 76.7 cikin ɗari na buƙatar ƙasar a zangon farko na 2026, idan aka kwatanta da kashi 45 cikin ɗari a daidai wannan lokaci na shekarar 2025. Wannan na nuna irin tasirin da matatar Dangote ke yi wajen ƙarfafa tsaron makamashi da kuma samar da kuɗaɗen shiga na ƙasashen waje.
