Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da shirin kara yawan jarin da kamfaninsa ke zubawa a kasar Habasha daga dala biliyan 2.5 zuwa sama da dala biliyan 4, domin karfafa masana’antu da samar da wadataccen abinci a Afirka.
Dangote ya bayyana hakan ne a garin Gode da ke yankin Somali na Habasha yayin wata ziyara da Firaministan kasar, Abiy Ahmed, ya shirya masa, inda suka duba aikin gina wata masana’antar taki da ake yi a yankin.
Sabbin ayyukan da za a aiwatar sun hada da bututun iskar gas mai tsawon kilomita 110, tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 120, masana’antar hada kayan marufi na polypropylene, da kuma masana’antar hada taki ta NPK mai karfin tan miliyan biyu a shekara, tare da wasu karin ayyuka.
A cewar Aliko Dangote, “Afirka na da dimbin damar noma, amma har yanzu nahiyar na fama da karancin abinci saboda rashin wadataccen taki. Ta hanyar wadannan zuba jari, muna da niyyar canja wannan hali ta hanyar kara yawan amfanin gona, tallafa wa manoma da kuma samar da dorewar wadatar abinci.”
Ya kara da cewa Afirka na da damar ciyar da kanta har ma ta rika fitar da kayayyakin noma zuwa kasashen waje idan aka kara zuba jari a bangaren taki da ababen more rayuwa.
Dangote ya bayyana cewa Habasha yanzu ita ce kasa ta biyu mafi girman karbar jarin rukunin kamfanonin Dangote a Afirka, inda ake sa ran za ta rike kusan kashi 9 cikin 100 na dukkan jarin kamfanin a nahiyar nan da shekarar 2030.
Ya yabawa Abiy Ahmed bisa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ke yi, yana mai cewa, “Firaministan na jagorantar ci gaba fiye da yadda ake zato, amma irin wannan ci gaba na bukatar hadin gwiwa mai karfi daga bangaren masu zaman kansu. Muna alfahari da hadin gwiwa da Habasha wajen gina daya daga cikin tattalin arzikin da zai fi bunkasa a Afirka cikin shekaru goma masu zuwa.”
Shi ma Abiy Ahmed ya bayyana Dangote a matsayin amintaccen abokin hulda, yana mai cewa aikin masana’antar taki zai rage dogaron Habasha ga shigo da taki daga kasashen waje, tare da tallafa wa miliyoyin manoma, samar da ayyukan yi da kuma karfafa matsayin kasar a matsayin cibiyar masana’antun noma.
Ya ce, “Irin wannan babban zuba jari na nuna karfin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu. Kara fadada irin wadannan kawance zai taimaka wajen habaka tattalin arziki, jawo karin masu zuba jari da kuma inganta rayuwar jama’a.”
