Bankin Duniya ya rage shirin bayar da tallafi ga Babban Bankin Najeriya (CBN) daga dala miliyan $10.5 zuwa dala miliyan $6.8, inda aka tsara a duba shirin a gaban kwamitin gudanarwa na bankin a ranar 27 ga Maris, 2026.
Tallafin, wanda ba rance ba ne, zai taimaka wajen aiwatar da CBN Technical Assistance Facility, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa tsarin sa ido na bankin ta hanyar fasahar zamani da bayanai (data-driven supervision) a fannin bankuna, tare da inganta kula da tsarin biyan kuɗi da aikawa da kuɗaɗe (remittance).
Sabbin bayanai daga shafin yanar gizon Bankin Duniya sun nuna cewa shirin ya kai matakin decision meeting, wato mataki na ƙarshe kafin amincewar kwamitin gudanarwa. Wannan na nuna ci gaba daga matakin duba ra’ayi (concept review) da aka ruwaito a watan Afrilu na 2025.
Za a ɗauki dukkan dala miliyan $6.8 ɗin ne daga Finance for Development Multi-Donor Trust Fund, ba tare da sa hannun International Development Association (IDA) ko International Bank for Reconstruction and Development (IBRD) ba.
Hakan ya tabbatar da cewa shirin ba zai ƙara wa Najeriya bashin waje ba.
Bankin Duniya ya bayyana cewa irin wannan sauyi abu ne da aka saba gani yayin shirye-shiryen aiwatar da ayyuka.
“Har sai kwamitin Bankin Duniya ya amince, abubuwa kamar tsari, sassa da girman kuɗaɗen da za a bayar na iya sauyawa ko a gyara su,” wani tushe ya shaida wa jaridar The PUNCH.
Idan aka amince da tallafin, zai ƙarfafa haɗin gwiwa da ke mayar da hankali kan haɗa kayan aiki na zamani da ilimin kimiyyar bayanai (data science) cikin ayyukan kula da harkokin kuɗi na CBN, domin tinkarar haɗurran da ke tasowa a tsarin kuɗin Najeriya.
An sanya shirin a matsayin mai matsakaicin haɗarin muhalli da zamantakewa, kuma ana sa ran zai ƙare a ranar 28 ga Fabrairu, 2029.
Bankin Duniya shi ne mafi girman mai ba Najeriya bashi, inda bashinsa ya kai dala biliyan $19.39, wanda ke wakiltar kashi 41.3 cikin ɗari na jimillar bashin waje na ƙasar.
Tsakanin shekarun 2023 da 2025, ana hasashen rancen da Najeriya za ta karɓa zai kai dala biliyan $9.65, wanda zai tashi zuwa dala biliyan $9.77 idan aka haɗa tallafi.
Jami’ai sun ce tallafin zai taimaka wajen zamanantar da ƙarfin sa ido na CBN, ƙarfafa kula da tsarin biyan kuɗi, da tabbatar da kwanciyar hankalin tsarin kuɗin Najeriya ba tare da ƙara nauyin bashi ba.

