Matattun Mai Sun Jawo Asarar ₦13 Tiriliyan ga Najeriya a Shekaru Biyu

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), ya kashe kimanin ₦13.2 tiriliyan kan matatun mai guda uku mallakin gwamnati tsakanin shekarun 2023 da 2024, duk da cewa matatun ba su yi aiki yadda zai zama riba a kasuwanci ba.

Bayanan da ke cikin rahoton kuɗaɗen NNPCL na shekarar 2024 sun nuna cewa matatun Port Harcourt, Warri da Kaduna sun ci bashin kamfanin har ₦4.52 tiriliyan a 2023 da kuma ₦8.67 tiriliyan a 2024. Wannan ya haɗa da kuɗaɗen da aka bayar don gyaran matatun (turnaround maintenance), gudanar da ayyuka da kuma kuɗaɗen banki.

Babban Daraktan Gudanarwa na NNPCL, Bayo Ojulari, ya amince cewa matatun sun zama “babbar asara” ga Najeriya. “Muna ta ɓata kuɗi kawai. Zan iya faɗar hakan da cikakken tabbaci yanzu,” in ji shi a Taron Koli na Makamashi na Ƙasa (Nigeria International Energy Summit) na 2026 da aka gudanar a Abuja.

Matatar Port Harcourt ce ta fi ɗaukar nauyi, inda bashinta ya tashi daga ₦1.99 tiriliyan a 2023 zuwa ₦4.22 tiriliyan a 2024.
Bashin matatar Warri ya ƙaru daga ₦1.17 tiriliyan zuwa ₦2.06 tiriliyan, yayin da na Kaduna ya tashi daga ₦1.36 tiriliyan zuwa ₦2.39 tiriliyan a wannan lokaci.

Ojulari ya bayyana cewa ana yawan tura danyen mai zuwa matatun, amma duk da haka matakin amfani da su bai wuce kashi 50 zuwa 55 cikin ɗari ba.
“Muna kashe kuɗi da yawa kan gudanar da ayyuka da kuma ’yan kwangila. Amma idan aka duba a ƙarshe, abin da muke yi shi ne zubar da darajar arziki,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa rashin ingantaccen shirin farfaɗo da matatun ne ya sa shugabancinsa ya dakatar da ayyukansu.

“Wani lokaci ana iya yin asara yayin zuba jari, amma kana da hangen dawo da riba a gaba. Wannan hangen ba a gan shi a nan ba,” Ojulari ya bayyana.
Matatun sun taɓa koma wa aiki a ƙarƙashin tsohon GCEO, Mele Kyari, a ƙarshen 2024, amma aka sake rufe su cikin ’yan watanni kaɗan.

Masu sukar lamarin, ciki har da Alhaji Aliko Dangote da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, sun yi nuni da cewa watakila matatun ba za su taɓa yin aiki yadda ya kamata ba duk da biliyoyin kuɗin da aka riga aka kashe.

Sai dai Ojulari ya ƙi amincewa da kiran a sayar da matatun, yana mai jaddada cewa har yanzu akwai yiwuwar farfaɗo da su. Yanzu ’yan Najeriya na jiran gani ko shugabancinsa zai iya sauya akalar kadarorin da aka dade ana kallon su a matsayin magudanar zubar da arzikin ƙasa.