CAC Ta Cire Fiye da Kamfanoni 400,000 Marasa Aiki Daga Rajista a 2025

Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni ta Ƙasa, Corporate Affairs Commission (CAC), ta bayyana cewa ta cire fiye da kamfanoni 400,000 da ba sa aiki ko kuma ba sa bin ƙa’ida daga kundin rajistar kamfanonin ƙasa a shekarar 2025.

Babban Magatakardar CAC, Husseini Magaji, ya bayyana hakan ne yayin wani Walk da hukumar ta shirya a ƙarshen mako a Abuja.

Ya ce a cikin shekarar 2025 kaɗai, “hukumar ta soke rajistar fiye da kamfanoni 400,000,” a matsayin wani mataki na tsaftace bayananta daga kamfanoni marasa aiki da waɗanda ba sa bin dokoki.

Shugaban CAC ya ƙara da cewa matakin ya kuma kasance domin kare inganci da amincin kundin rajistar kamfanonin ƙasa.
“A yau, CAC na bayar da ayyuka ko’ina, a kowane lokaci, kuma awanni 24 a rana. Za ka iya rajistar kasuwancinka daga ɗakinka ba tare da zuwa ofisoshinmu ba,” in ji Magaji.

Magaji ya kuma bayyana cewa CAC, tare da haɗin gwiwar Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Kasuwanci ta Najeriya (SMEDAN), ta sauƙaƙa rajistar kasuwanci kyauta ga ’yan kasuwa 250,000, a wani ɓangare na tallafin da take bai wa ƙananan kasuwanci a faɗin ƙasar.