Kotun ta kori karar APC da ke neman hana kananan hukumomin Kano kudade Gwamnatin Tarayya
Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar, tana neman dakatar da rarraba kudaden gwamnatin tarayya ga kananan hukumomi 44 na jihar Kano da ke karkashin shugabancin jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP). Karar, wadda aka shigar tun watan Nuwamba 2024, ta fito…

