Kwankwaso Ya Ziyarci Fadar Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Bola Tinubu Tare da Rabiu Musa Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an hangi zuwansa a Dakin Tarbar Banquet na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.

Kwankwaso ya halarci taron Nigeria Forest Economy Summit 2025 wanda Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Haɗa-hadar Tattalin Arziki da Ƙarfafa Shiga Jama’a cikin Tattalin Arziki (PreCEFI) ya shirya.

Sai dai Kwankwaso bai gabatar da jawabi a wajen taron ba, haka kuma bai yi magana da manema labarai ba yayin da ya halarci taron.

A yayin taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa – wanda Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Hadejia, ya wakilta – ya yi gargaɗi dangane da mummunan halin da dazukan Najeriya ke ciki da kuma barazanar tattalin arziki da hakan ke haifarwa idan ba a dauki matakin gaggawa ba.