Babangida Ya Karyata Jita – Jita Cewa Ya Ƙi Karɓar Naɗin da Tinubu Yayi Masa

Mahammed Babangida

Dan tsohon shugaban ƙasa na mulki soja, Mahammed Ibrahim Badamasi Babangida (rtd), ya nesanta kansa daga rahotannin da ke yawo cewa ya ƙi karɓar naɗin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa.

A wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa, Babangida ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya marar tushe, yana mai jaddada cewa bai taɓa ƙin karɓar wani girmamawa ko naɗi daga gwamnatin Tinubu ba.

Ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita da ke ƙoƙarin jefa rudani a tsakanin al’umma da shugabanni.