A ci gaba da bikin makon ‘yan jarida na shekarar 2025. Yan jarida ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Babban Birnin Tarayya (FCT), sun gudanar da tattaki na lumana domin goyon bayan ‘yancin faɗar albarkacin baki, dimokuraɗiyya da kuma kare ƴancin ƙafofin yaɗa labarai a ƙasar.
Da take jawabi ga manema labarai yayin zanga-zangar, Shugabar NUJ reshen FCT, Grace Ike, ta bayyana cewa wannan tafiya alama ce mai ƙarfi cewa ‘yancin faɗar albarkacin baki ginshiki ne na kowace dimokuraɗiyya mai ƙarfi, kuma ƙafofin yaɗa labarai a Najeriya suna ci gaba da zama masu tsayawa tsayin daka wajen kare gaskiya da kare dimokuraɗiyya.
“Ba tare da ‘yancin faɗar albarkacin baki ba, al’umma za ta yi shiru, muryoyi za su yi gum, kuma neman gaskiya zai kasance mafarki mai nisa. Aikin jarida yana ɗauke da harshen wuta da ke haskaka hanyar kyakkyawan mulki, riƙon amana da kare haƙƙin ɗan adam,” in ji ta.
Ta bayyana cewa duk da ƙalubalen tattalin arziki da barazanar da ke kara ƙaruwa ga aikin jarida, ƴan jarida a Najeriya ba za su lamunci cenzura, tsoratarwa ko cin zarafi ba, kuma za su ci gaba da rike masu iko da alhaki, kare marasa ƙarfi da kuma kare muradun jama’a.
Grace Ike ta nemi a duba lafiyar ‘yan jarida, a basu ingantaccen yanayin aiki, tare da ganin cewa an ɗauke su a matsayin ma’aikata na gaba-gaba wajen neman gaskiya, adalci da cigaban ƙasa.
“Dole ne a samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ƴan jarida domin ba su masu roƙo ba ne. Wadanda ke fuskantar haɗari don kare gaskiya da martabar aikin jarida, su ma suna da haƙƙin a kula da su yadda ya kamata,” in ji ta.
Ta bayyana taken zanga-zangar na bana, “Tafiya Don Kare ‘Yancin Jarida” a matsayin hujjar da ke ƙarfafa matsayin ‘yancin faɗar albarkacin baki a matsayin ginshiƙi ga sauran haƙƙin ɗan adam. Ta kuma bukaci ƴan jarida da su kasance masu daidaito, riƙon amana, kauce wa yaɗa ƙarya da rungumar sabbin fasahohin zamani cikin natsuwa da ƙwarewa.
“Dole ne mu tsaya tsayin daka don kare ƙa’idojin aikin jarida. Saboda haka, muna cewa: babu yarda da tsoratarwa, babu yarda da cin zarafi, babu yarda da cenzura. NUJ FCT ta tsaya kai da fata wajen cewa ba za mu yi shiru ba!
Za mu ci gaba da kare sararin kafafen yaɗa labarai da ke mutunta ‘yancin ‘yan jarida, da goyon bayan dimokuraɗiyya tare da ba kowace murya dama. Ina so in jaddada cewa ‘yancin jarida ba abin tattaunawa ba ne,” in ji ta.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban NUJ FCT, Ndambabo Yahaya, ya bayyana cewa zanga-zangar na da nufin ɗaga murya kan muhimmancin ‘yancin ‘yan jarida a Najeriya.
“Muna son mu ɗaga muryar mu kan ‘yancin ‘yan jarida a matsayin haƙƙi, ba wata kyauta ba, domin shi ne mahaifin sauran haƙƙin bil’adama,” in ji shi.
Ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen kare wannan haƙƙi da kuma tabbatar da cewa ‘yancin jarida yana da tushe mai ƙarfi a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.
