Shugaban Kasar Gambiya Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Gidan Marigayi Buhari a Daura
Shugaban Kasar Gambiya, Adama Barrow, a ranar Juma’a ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a garinsa na Daura, Jihar Katsina. Shugaba Barrow, wanda ya isa Katsina don ziyarar ta’aziyyar, ya samu tarba daga Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, tare da wasu daga cikin ‘yan uwan marigayi Buhari….

