Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ta fuskanci wani cikas daga jami’an shige da fice a safiyar Alhamis a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, yayin da take kokarin hawa jirgi zuwa Birtaniya.
A cewar rahotanni, an dakatar da ita daga tafiya ne saboda sunanta ya bayyana a jerin wadanda ake sa ido a kansu (watch list), kuma hakan na iya zama bisa bukatar wasu daga cikin shugabannin Majalisar Tarayya.
Wani dan uwanta da ya san da lamarin ya shaida cewa Sanata Natasha tana tafiya tare da mijinta domin halartar bikin yaye dansa a kasar Birtaniya, amma sai jami’an shige da fice suka dakatar da ita a mashigar tashin jirage.
“An shaida mata cewa an bukaci a sanya sunanta a cikin jerin wadanda ake sa ido saboda tana da yiyuwar yin gudun hijira, kamar yadda shugabannin Majalisar Tarayya suka bukata,” in ji dan uwan nata, wanda ya nemi a boye sunansa saboda dalilan tsaro. “Muna mamakin dalilin wannan tsangwama, musamman ganin cewa babu wata hukuncin kotu da ke hana ta fita daga kasar, kuma ba ta taba kaucewa kiran kotu ba.”
Wannan lamarin da ya jawo hankalin jama’a a filin jirgin sama, na zuwa ne a daidai lokacin da ke akwai takaddama tsakanin Sanata Natasha da shugabancin Majalisar Dattawa.
A kwanakin baya, an dakatar da Sanata Natasha daga mukaminta a majalisa bayan ta yi korafi kan sauya wurin zama da aka yi mata. Daga bisani, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da yi mata cin zarafi ta hanyar lalata (sexual harassment) — zargin da Akpabio ya musanta da karfi.
Har ila yau, Gwamnatin Tarayya ta shigar da kara biyu na cin mutunci da suka shafi laifin shari’a a kan Sanata Natasha. Ita kuwa ta yi zargin cewa ana kullawa makirci ne daga cikin majalisa domin bata mata suna, kuma wasu daga cikin mukarrabanta sun alakanta abin da ya faru da ita a filin jirgin sama da wannan rikicin siyasa.
Wasu shaidu sun ce Sanatar ta yi ta kiran wayar gaggawa zuwa ga manyan jami’an gwamnati da na shige da fice domin neman a warware lamarin. Bayan kusan awa guda, an ba ta izinin hawa jirgin na kamfanin British Airways.
“An buga mata tambarin fita a fasfota, kuma daga nan aka ba ta damar wucewa,” in ji wani shaidan gani da ido.
Sanata Natasha ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ki bayar da cikakken bayani, tana cewa: “Jirgi na dab da tashi.”
Dan uwanta ya bayyana fatan cewa za a guji maimaita irin wannan matsala da zarar ta dawo gida daga tafiyarta cikin makonni biyu masu zuwa.



