Shahararren gwarzon wasan kwaikwayo na dambe (wrestling), Hulk Hogan, ya rasu yana da shekaru 71, kamar yadda TMZ Sports ta ruwaito.
An kira gaggawa da misalin safiyar Alhamis zuwa gidansa da ke Clearwater, Florida, bayan da aka bayyana wani lamari na “kamawar zuciya” (cardiac arrest).
Ganau sun ce an hango motocin ‘yan sanda da na agajin gaggawa (EMT) da dama a wajen, inda aka ga Hogan a kan gadon daukar marasa lafiya aka saka shi cikin motar asibiti.
Kwana kadan kafin rasuwarsa, matar sa Sky ta bayyana cewa rade-radin da ke yawo a intanet na cewa mijinta yana cikin kwanciyar rashin sani (coma) ba gaskiya ba ne. Ta jaddada cewa zuciyarsa na da karfi kuma yana murmurewa daga wasu tiyata da aka masa.
An haifi Hulk Hogan da suna Terry Bollea, kuma ya taka rawar gani wajen sauya wasan dambe daga wasa na musamman zuwa wani babban shahararren shirin nishaɗi na duniya baki ɗaya. Kafin shahararsa, wasan dambe bai da dimbin masoya. Amma saboda salo, karfin hali, da kuma kamannin jarumi da yake da shi, Hogan ya zama fuskar WWE a shekarun 1980, inda ya ja hankalin miliyoyin masoya – yara da manya.
A shekarar 1996, Hogan ya sake sunansa zuwa “Hollywood Hogan” kuma ya sauya matsayinsa daga jarumi zuwa mugun dan wasa, inda ya kafa kungiya mai suna New World Order (NWO). Wannan mataki ya farfado da aikinsa kuma ya kara daukaka wasan dambe.
An fara shigar da shi cikin WWE Hall of Fame a 2005, amma aka fitar da sunansa a 2015 bayan fitar wani bidiyo da aka dauka a boye inda ya furta kalaman wariyar launin fata. Daga bisani ya kai kara kotu kan kafar yada labarai ta Gawker wacce ta fitar da bidiyon, kuma ya lashe shari’ar. WWE ta dawo da sunansa a 2020 kuma aka sake shigar da shi cikin Hall of Fame – a karo na biyu a matsayin memba na NWO.
Bayan wasan dambe, Hogan ya yi fice a fagen fim. A shekarar 1982 ya fara fitowa a fim din Rocky III a matsayin Thunderlips, sannan ya fito a wasu fina-finai kamar No Holds Barred, Suburban Commando, da Mr. Nanny. A shekarun 2000, ya kuma shiga harkar reality TV a cikin shirin Hogan Knows Best da ke kan tashar VH1 wanda ya dinga nuna rayuwar iyalinsa – matarsa Linda da yaransu Nick da Brooke.
Gado da tasirin Hulk Hogan a fagen wasan dambe da al’adu zai dade yana cikin tarihi, kuma za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin gwarzo kuma jarumi na nishaɗin wasanni.
