Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a matsayin mafi karfin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2027.
Lamido ya shawarci PDP da ta dauki matakan musamman don dawo da shi cikin jam’iyyar, yana mai cewa babu wani dan PDP daga kudu da zai iya kai wa Jonathan a fannin kwarewa da gogewa.
Yayin hira da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV, Lamido ya ce:
“Ina ganin PDP yanzu ya kamata su nemi Jonathan sosai. Shi ne zabinsu mafi kyau. Duk wanda PDP ta tsayar, ‘yan Najeriya za su goyi bayansa.”
Ya bayyana Jonathan a matsayin shugaba wanda ya taba jagorantar kasa, yana fahimtar tafiyar da gwamnati, kuma yana iya yin aiki tare da kowa cikin lumana.
Ya kara da cewa:
“Shi ne mafi maraba, mai kwarewa kuma mai cancanta. A ganina, cikin PDP yanzu, da girmamawa ga dukkan mambobi, ban ga wanda ya fi Jonathan ba idan har zai dawo PDP. Idan za a ba kudu mulki a PDP, wa ne zai iya kalubalantar Jonathan wajen gogewa, jagoranci, iya sauraro, da kuma kasancewa jagora mai son hadin kai?”
Haka kuma Lamido ya bukaci a kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da sauran mambobin PDP da suka yi aiki tare da APC a zaben 2023.
“Dukkan wadannan ‘yan jam’iyya masu laifi su Wike, su Ortom, su Ikpeazu, da sauran wadanda suka fito fili suka yi kamfen kan PDP a 2023 kuma suke cewa za su yi aiki da APC a 2027 ya kamata a kore su daga jam’iyya,” in ji shi.
Lamido ya kuma nuna takaicinsa kan “dogon tarihi na rashin ladabi da biyayya a cikin jam’iyyar,” yana mai cewa lokaci ya yi da za a aiwatar da matakan ladabtarwa.
Ya ce:
“Tun bayan zaben fidda gwani na 2022 zuwa zaben 2023, akwai mutane da saboda bukatunsu da son zuciyarsu suka fusata da abin da ya faru a taron jam’iyyar. Suka juya suka yi wa jam’iyya adawa. Mun sha fama da irin wannan matsala – wato rashin ladabi da cin zarafin jam’iyya.”
Wannan jawabi na Lamido ya biyo bayan sabon yunkuri a cikin PDP na neman Jonathan domin 2027, wanda ya dauki hankalin kasa baki daya.
A watan Agustan 2025, manyan jiga-jigan jam’iyyar sun tabbatar da ana ci gaba da tattaunawa da tsohon shugaban kasa don ya zama dan takarar jam’iyyar. Wannan na zuwa ne bayan shawarwari na ciki da kuma kira daga wasu manyan mambobi wadanda ke ganin cewa kwarewarsa a fannin mulki, farin jini a kasa, da nagartar jagoranci na ba PDP damar dawo da mulki.
Jonathan, wanda ya jagoranci Najeriya daga 2010 zuwa 2015, har yanzu yana daga cikin fitattun ‘yan siyasa a kasar. Duk da cewa bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, matarsa, Patience Jonathan, kwanan nan ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu, inda ta ce ba za ta tsaya takara da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ba.

