A wani lokaci da Najeriya ke mai da hankali kan bukatar matasa su mallaki sana’o’i a tare da takardun shaidar karatu, mutane irin su Muhammad Abdullahi ba wai kawai sun kware a sana’a ba, har ma suna horas da wasu a fagen da suke yi.
Muhammad makaniƙin mota ne dan asalin unguwar Gulde a karamar hukumar Biu, Jihar Borno. Bayan ya koyi gyaran mota a garinsu, yanzu yana aiki ne a Dawaki, karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Tare da shekaru masu yawa na gogewa, Muhammad yana horas da matasa 15 a matsayin ɗalibansa, tare da burin zama daya daga cikin manyan ƙwararrun makaniƙan mota a Najeriya.
Farkon Tafiya da Dalilin Farawa
Muhammad ya bayyana yadda ya fara koyon sana’ar yana da kimanin shekara 10, kuma tun sama da shekaru 25 yana cikinta har ya zama uba da ginshiki ga iyalinsa da abokansa.
“Kakannina ne suka fara zaburar da ni a wannan sana’a tun ina dan shekara 10. Sun ga yadda nake bata lokaci bayan dawowa daga makaranta, sai iyayena suka ba su shawarar su saka ni in fara koyon gyaran mota.
“Da farko na yi ƙoƙarin guje wa hakan, na ce ban ma san abin da ake kira ‘spana’ ba, amma na karfafa gwiwa da tunanin cewa kowanne ƙwararre ya fara daga koyon sana’a. Yau ina alfahari da abin da na zama, saboda ta wannan sana’a nake tallafa wa iyali da abokai,” inji shi.
Hanyar zuwa Abuja da Kalubale
Matashin makaniƙin ya ce bayan ya kware sosai, wani abokinsa ya karfafa masa gwiwar barin garinsu zuwa babban birnin tarayya domin samun damar yin sana’a a wuri mafi arziki, amma hakan bai zo da sauƙi ba.
“Abokina wanda shima makaniƙi ne a Abuja ya ga ƙwarewata ya ce in zo. A lokacin na shiga tunani kan yadda zan rayu a gari da ban san kowa ba, amma godiya ga Allah, duk hakan tarihi ne yanzu.
“Muna zuwa Abuja muka hadu da babban mai sana’ar, amma na fuskanci cikas saboda sai na kawo uba ko wanda zai ba shi tabbacin halayyata kafin ya karɓe ni. Daga baya na shawo kan matsalar, aka ba ni wurin zama sannan na fara kasuwancina a nan Abuja,” inji shi.
Muhammad ya tuna daya daga cikin aikin da ya fi wahala a FCT: “Na taba daukar watanni biyu ina gyaran Mazda 2009. Aikin ya yi wahala saboda wani makaniƙi ya taba aikin ya kuma jawo karin matsala. Duk da hakan, na koyi darasi mai mahimmanci.”
Motoci Masu Lantarki: Bin Cigaba
Masana’antar motoci tana canzawa da sauri saboda ci gaban fasaha kamar wutar lantarki, tuƙi ta atomatik, haɗaɗɗen sadarwa, da amfani da ingantattun manhajojin kwamfuta. Wannan na nufin makaniƙan mota a cikin gida suna bukatar sabunta iliminsu akai-akai, kuma Muhammad da tawagarsa na yin hakan.
“Da farko lokacin da muka fara karɓar motoci masu sarrafa kansu domin gyara, ba mu da ƙwarewar da ake bukata. Sai muka kawo ƙwararru don su koya mana, daga nan muka samu ilimi mai yawa. Yanzu muna da tabbacin iya gyara su mu kadai,” inji Muhammad.
Gargaɗi da Shawara
Makaniƙin mota ya gargadi matasa su daina son samun kuɗi cikin gaggawa, su tashi su nemi halal.
A cewarsa, “Kuɗi suna da muhimmanci a rayuwa, amma matasa su gane cewa samun sa yana bukatar aiki tukuru da jajircewa, ba ya zuwa cikin sauƙi. Dole mu yi halal domin samun kuɗi.”
Muhammad ya kuma shawarci masu motoci da “su kula da yadda suke amfani da motocinsu, domin hakan zai ƙara tsawon lokacin amfani da motar, tare da kare rayuka.”

