By Idris Sultan
An shawarci matasan Najeriya da su kasance masu jajircewa domin cimma burinsu, domin wariya ko asalin mutum ba su zama abin da zai hana nasara ba.
Wannan shawarar ta fito ne daga wani mai amfani da kafar sada zumunta, wanda ya bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne niyyar koyo da sha’awar kara inganta kai a kowace rana.
Ya ce, “Nafisa ta wakilci mafi kyawun abin da harshen Turanci zai iya zama, ta lashe gasar World English Competition. Wannan ba wai kawai nasara ba ce, abin tunawa ne cewa kada a bar wariya ta zama mai tsara labarinka.
“Kada ka bari wani ya gaya maka abin da za ka iya ko ba za ka iya yi ba. Asalinka ba shi ne iyakarka ba, shi ne karfinka. Ga kowanne matashi da aka ce ba ka isa ba saboda inda ka fito, ka tuna da wannan: girma ba shi da lasisi na murya ko yare.
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne niyyar koyo, sha’awar bunkasa kanka, da jarumtar tashi tsaye,” in ji shi.
Wannan shawarar ta fito ne bayan Nafisa Abdullahi Aminu, daliba ‘yar Najeriya mai shekara 17, ta zama zakarar duniya a fannin harshen Turanci a gasar 2025 TeenEagle Global Finals da aka gudanar a birnin London, Birtaniya.
Nafisa, dalibar makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC) da ke Jihar Yobe, ta doke sama da mahalarta 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen da Turanci ne harshen su na uwa, domin lashe kambun.
Sauran daliban Najeriya da suka lashe kambun a wannan gasa sun hada da Rukayya Muhammad Fema, mai shekara 15, wadda ta zama Zakara Ta Duniya a muhawara (Overall Best in Debate), da kuma Hadiza Kashim Kalli, wadda ta samu lambar yabo ta hazaka (Outstanding Talent Award – Gold Medal).
