Yaki da Yunwa: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Bankin Abinci na Ƙasa

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Bankin Abinci na Al’umma na Ƙasa domin yaƙi da yunwa da rashin gina jiki, musamman ga yara ‘yan ƙasa da shekara shida, mata masu juna biyu, da masu shayarwa.

An ƙaddamar da shirin ne a Abuja ta hannun Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, wadda ta ƙaddamar da kwamitin amintattu tare da bayar da gudummawar Naira miliyan 500, tana kira ga ‘yan Najeriya, kamfanoni da sauran abokan hulɗa su mara wa shirin baya.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da yawan matsalar rashin gina jiki a duniya, inda kusan ɗaya cikin uku na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar ke fama da matsalar.

UNICEF ta kiyasta cewa kimanin yara miliyan biyu na fama da matsanancin rashin gina jiki, amma kashi 20 cikin 100 ne kaɗai ke samun magani.

Ministan Lafiya mai kula da harkokin haɗin gwiwa, Muhammad Ali Pate, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na “Renewed Hope Agenda,” yana mai jaddada muhimmancin abinci mai gina jiki ga lafiyar jama’a da rayuwar yara.
Ya bayyana cewa an amince da asusun Naira biliyan 7 domin sayo abinci daga cikin gida ta hanyar tsarin al’umma.

Pate ya kuma ce masu bayar da gudummawa da ba a bayyana sunayensu ba sun bayar da dala 500,000, yayin da manyan gudummawa suka fito daga Dangote Foundation (Naira biliyan 20 cikin shekaru biyar) da Nigerian National Petroleum Company Limited (Naira biliyan 10 cikin shekaru biyar).

Gwamnonin jihohi sun yi alƙawarin bayar da gudummawar da ta dace, inda gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa tsaron abinci muhimmin ginshiƙi ne ga haɓakar tattalin arziki da zaman lafiya.

Babban Daraktan National Primary Health Care Development Agency, Muyi Aina, ya ce za a tantance gidaje masu buƙata ta hanyar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 30,000, ta amfani da tsarin rajista na zamani.

Za a bai wa masu cin gajiyar shirin takardun shaida (vouchers) da za su iya amfani da su a bankunan abinci da ke kusa da cibiyoyin lafiya.

Za a fara aiwatar da shirin a matakai a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar, inda ake sa ran za a kai ga gidaje sama da 500,000 a shekarar farko, tare da tsauraran matakan sa ido da Bank of Agriculture zai kula da su.