Dietician: ‘Yar Najeriya ta Rasa Lasisi a Birtaniya Saboda Amfani da ChatGPT

Wata ma’aikaciyar lafiya ‘yar Najeriya, Aiwanehi Aigbokhaevbo, ta rasa lasisinta na aiki a Birtaniya bayan an same ta da amfani da ChatGPT yayin wata hira ta neman aiki da aka yi daga nesa.

Aigbokhaevbo, wadda ke da rajista a matsayin dietician a Birtaniya, ta nemi aikin dietician na masu cutar daji (oncology) a asibitin Royal Surrey County Hospital a watan Maris 2024. An gudanar da hirar ne ta manhajar Microsoft Teams yayin da take a Najeriya.

Mambobin kwamitin hira sun lura cewa tana yawan roƙon a maimaita tambayoyi, sannan ta kan sake faɗin tambayar kafin ta ba da amsa.

An bayyana amsoshinta a matsayin masu santsi, cike da cikakkun bayanai, kuma kamar na littafi, tare da amfani da kalmomin likitanci na matakin da ya wuce abin da ake tsammani.

Kwamitin ya ce: “Amsoshin da ta bayar sun kasance kamar daga littafi, suna nuna ƙwarewa da ilimi na musamman a mataki mai zurfi.”

Haka kuma sun lura da yadda idanunta ke motsawa gefe zuwa gefe, abin da ya nuna kamar tana karantawa daga wani allo.

Bayan hirar, ta gabatar da wani bincike (case study) na mintuna 45, wanda kwamitin ya yanke hukuncin cewa an shirya shi ne da taimakon na’urar basira (AI), saboda cikakken bayaninsa.

A lokacin sauraron ƙarar, Aigbokhaevbo ta musanta amfani da AI, tana cewa ta kan maimaita tambayoyi ne don tabbatar da fahimta, yayin da kallon gefe ya kasance don duba haɗin intanet.

Sai dai Health and Care Professions Tribunal Service ya ce bayananta ba su dace ba, yana mai nuni da rashin nadama da fahimtar kuskuren da ta aikata.

Hukumar ta ce: “Duba da halin da ta nuna da kuma rashin wata alamar nadama ko gyara, akwai yiwuwar sake aikata irin wannan laifi.”
Sakamakon haka, an soke lasisinta tare da cire sunanta daga rajistar dieticians a Birtaniya.

Haka kuma an ɗora mata hukuncin dakatarwa na wucin gadi na watanni 18, wanda a cikin wannan lokaci tana da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.