Wani Soja Ya Kashe Dan Sanda Bayan Ya Soke Shi da Wuka a Jalingo

Wani sabon soja da aka dauka kwanan nan, mai suna Dauda Dedan, ana zarginsa da kashe wani dan sanda, Aaron John, wanda ke aiki da rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, ta hanyar soka masa wuka a Jalingo.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, James Lashen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jalingo a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa abin takaicin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare, a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, kusa da birnin Jalingo.

Lashen ya ce marigayin dan sanda, John, ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da wata takaddama da ta barke tsakaninsu da sojan, inda a yayin da yake kokarin shawo kan lamarin, sojan ya soka masa wuka.

PPRO din ya kara da cewa sojan ya tsere daga wurin bayan kisan, sai dai rundunar sojojin Najeriya ta riga ta fara bincike kan lamarin tare da tabbatar wa ‘yan sanda cewa za a kamo sojan domin fuskantar hukunci.

“Mun riga mun sanar da hedkwatar Rundunar Sojoji ta 6 Brigade game da lamarin, kuma mun samu cikakken tabbaci daga gare su cewa za su nemo sojan da ya tsere domin fuskantar doka,” in ji Lashen.

“Rundunar sojoji da ‘yan sanda suna aiki tare cikin fahimta. Mun riga mun kai gidan sojan domin gudanar da bincike, kuma za mu tabbatar an cafke shi tare da hukunta shi yadda ya dace.”

Lashen ya jaddada cewa dangantaka tsakanin rundunar sojoji da ‘yan sanda a jihar na da kyau sosai kuma babu wata sabani tsakaninsu.