Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kama dan gwagwarmaya kuma mai wallafa Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a babban ofishinta da ke Abuja, bayan ya amsa gayyatar da aka aika masa.
Sowore ya isa hedkwatar ‘yan sanda da misalin karfe 12 na rana a ranar Laraba dauke da jakar tafiya, kuma ba da jimawa ba aka tsare shi. A cewar rahoton Premium Times, rundunar ‘yan sanda ba ta bayyana takamaiman korafi ko kuma rubutacciyar kara da aka shigar a kansa ba.
Tun da farko, Sahara Reporters ta ruwaito cewa wasikar farko daga ‘yan sanda ta zargi Sowore da “tayar da hankalin jama’a.” Sai dai a ranar Litinin, an aike da sabuwar wasika ga lauyansa wadda ta sauya zargin zuwa na “jabun takardu da batanci na laifi.”
Kungiyoyin farar hula da suka hada da Amnesty International sun bayyana kama Sowore a matsayin “abin kyama da kuma wanda ke da niyyar siyasa,” tare da bukatar a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
“Amnesty International na Allah wadai da kama dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam kuma dan jarida, Omoyele Sowore, wanda ya dade yana fuskantar tsangwama da barazana daga rundunar ‘yan sanda. Gwamnatin Najeriya dole ta sake shi nan take ba tare da sharadi ba…” in ji Amnesty International Nigeria a shafinta na Twitter.
Tun daga shekarar 2019 ne aka fara cafke Sowore saboda ayyukan gwagwarmayarsa. A watan Nuwamba na shekarar 2019, Amnesty International ta ayyana shi a matsayin “Fursuna Saboda Ra’ayi” bayan kama shi kan zanga-zangar lumana da ya jagoranta.
A watan Janairu, Foundation for Investigative Journalism (FIJ) ta rahoto cewa ‘yan sanda sun bukaci Sowore ya mika fasfo dinsa na kasa da kuma samun jami’in gwamnati mai matakin aiki na 17 a matsayin mai tsaya masa kafin a sako shi.
Lauyoyinsa na shirin daukaka kara a gaban kotu kan wannan sabon kamawa, yayin da mabiya daga Take It Back Movement ke ci gaba da bukatar a sako shi.

