Sulhu da Yan Bindiga: Gwamnati Nigeriya ta Karyata El-Rufai

Mallam Nuhu Ribadu

Sabuwar cacar-baki ta kunno kai tsakanin Nasir El-Rufa’i da gwamnatin tarayya bayan tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin tare da zargin ta da ta’azzara matsalolin tsaro ta hanyar “ƙarfafa ƴanbindiga” maimakon ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya a sassan ƙasar.

El-Rufai ya yi zarge-zargen a zantawarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatin na taimakon ƴanbindigar ta hanyar ba su maƙudan kuɗaɗe ta bayan fage.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya take ta bayyana nasarorin da ta ce tana samu a yaƙin da take yi da ƴanbindiga da sauran matsalolin tsaro a ƙasar.

A ƴan makonnin baya ne gwamnatin ta sanar da wasu manyan nasarorin da ta ce ta samu a yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar, ciki har da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake zargi da kitsa hari kan gidan yarin Kuje, sannan kuma aka daɗe ana neman su ruwa a jallo.

Haka kuma gwamnatin ta sanar da kashe wasu jagororin Boko Haram, sannan ta sanar da ceto wasu mutane masu yawa daga hannun ƴanbindiga.