Masana’antar kafafen yaɗa labarai ta Najeriya ta shiga cikin alhini a ranar Litinin, bayan rasuwar mai gabatar da shirye-shirye kuma ’yar jarida ta tashar ARISE News Channel, Somtochukwu Christelle Maduagwu, wadda aka fi sani da Sommie.
An kashe Maduagwu a safiyar ranar 29 ga Satumba, 2025, a wani hari na fashi da makami a gidanta da ke unguwar Katampe, Abuja. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da kaddamar da bincike a kan lamarin.
Maduagwu, wadda ta ke da shekaru 29 kacal, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun masu gabatar da shirye-shirye a ARISE.
A cikin wata sanarwa da Hadiza Usman-Ajayi ta fitar a madadin hukumar gudanarwar ARISE News, an bayyana mamaciyar a matsayin “mace mai daraja a cikin iyalin ARISE News, kuma murya mai ƙarfi da ta riƙa jan hankali tare da haɗa kai da masu kallo.”
Baya ga aikin jarida, Maduagwu kuma lauya ce ta ƙwarai. Abokan aikinta sun bayyana ta a matsayin mai kwarewa, mai goyon baya, kuma mai sha’awar aikinta sosai.
Sanarwar ARISE ta ƙara da cewa: “Har yanzu muna cikin alhini, kuma muna kira ga hanzarta bincike, kama da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta’asa.” Haka kuma, hukumar ta mika ta’aziyya ga iyayenta, ’yan’uwanta, abokan arziki, da dukkan masoyanta.
An haifi Maduagwu ne a ranar 26 ga Disamba, 1995, kuma ta riga ta kafa suna a matsayin yarinya matashiya a fagen aikin jarida, inda ta samu girmamawa daga abokan aiki da kuma jama’a.
Rasuwarta ta haifar da rera-jin-jiki a tsakanin masana harkar kafafen yaɗa labarai da kuma fannin shari’a, inda da dama suka yi ta yabawa da jajircewarta da kuma irin gibin da mutuwarta ta haifar ga aikin jarida a Najeriya.
