Wata mata a jihar Bauchi ta mutu bayan ta cinna wa kanta wuta, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa matar ta kunna wuta a jikinta a cikin wani hali da bai bayyana ba, abin da ya ja hankalin mazauna unguwa da hukumomi.
Lamarin ya faru ne a wani yankin zama na jihar, inda mazauna wurin suka tarar da wutar tana ci, suka ruga domin taimaka mata.
Shaidu sun ce sun yi kokarin kashe wutar da kuma ba ta agajin gaggawa, amma konewar da ta samu ta yi tsanani.
An garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), amma ma’aikatan lafiya sun tabbatar da mutuwarta nan take saboda tsananin raunukan da ta samu.
Rahotanni na farko sun nuna cewa an gano wata takarda a wajen, sai dai ba a bayyana abinda ke cikinta ba ko kuma alaƙarsa da lamarin.
Hukumomi za su duba hoton CCTV, su yi hira da shaidu, tare da bibiyar matakan da ta dauka kafin faruwar lamarin domin samun ƙarin hujjoji.
Rundunar ‘yan sandan jihar na aiki tare da kwararrun likitoci da masu bincike domin samun cikakken haske kan lamarin.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, CSP Mohammed Wakil, ya bayyana cewa bincike na farko ya nuna matar tana fama da matsalar tabin hankali tun bayan haihuwar danta na ƙarshe.
