Kungiyar Gbenga Hashim Solidarity Movement (GHSM) ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ba zai samu “tikitin saukaka” na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP ba a zaben 2027.
Shugaban ƙasa na GHSM, Abdulrazaq Hamzat, ya yi wannan jawabi ne a matsayin martani ga furucin Farfesa Jerry Gana wanda ya nuna yiwuwar Jonathan zai dawo takara a ƙarƙashin PDP.
A cewarsa, “Tare da girmamawa, Farfesa Jerry Gana yana da ’yancin nuna farin cikinsa game da dawowar Jonathan. Amma fa, ’yan takarar shugaban ƙasa a PDP za su fito ne ta hanyar sahihin zaɓen fitar da gwani (primaries) da ya dace da dokar zaɓe ta 2022. Ƙarshe, Allah ne zai yanke hukunci, ba wasu kaɗan daga cikin jagororin jam’iyya ba.”
Hamzat ya ce, ’yan Najeriya suna neman cigaba, ba wai komawa baya ba, inda ya gargadi cewa Jonathan na wakiltar “tsohon zamani” da al’umma ke son barin shi a tarihi.
Ya ƙara da cewa, “Lokacin mulkin Jonathan ba za a iya cewa cikakken lokaci ne ba. A wancan lokacin an fara lalata haɗin kan ƙasar, an kuma sake hura wutar ƙabilanci da ƙiyayyar addini – wani abu da ya ƙara tsananta a mulkin da ya biyo baya.”
Game da harkar ƙasashen waje, Hamzat ya soki manufar gwamnatin Jonathan wacce ta goyi bayan shigar NATO a cikin rikicin Libya a 2011, duk da matsayar kungiyar Tarayyar Afirka (AU). Ya bayyana wannan mataki a matsayin “babban kuskure” da ya lalata yankin Sahel, ya kuma tsananta matsalar tsaro a Najeriya, Mali, Chadi, Nijar, Burkina Faso da sauran ƙasashen Yammacin Afirka.
A cikin gida kuwa, shugaban GHSM ya ce har yanzu Jonathan bai amsa tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da suka biyo bayan mulkinsa ba, musamman badakalar Dasukigate ta makudan kuɗaɗen siyan makamai.
Duk da haka, Hamzat ya jaddada cewa PDP jam’iyya ce ta dimokuraɗiyya, kuma babu wani ɗan takara – ko da tsohon shugaban ƙasa ne – da zai sa ran samun tikitin jam’iyya kai tsaye.
Ya ce, “Idan Jonathan na son dawowa Aso Rock, dole ne ya fito ya fafata da ’yan takarar da ke da hangen nesa na haɗa kan ƙasa irin su Dr. Gbenga Olawepo-Hashim, ta hanyar sahihin zaɓen fitar da gwani.”
Hamzat ya ƙara da cewa, ’yan Najeriya suna buƙatar sabuwar shugabanci da sabon hangen nesa don magance ƙalubalen ƙasa, inda ya jaddada cewa, “hanya ɗaya tilo zuwa gaba ita ce gaba, ba baya ba.”
