Imam Abubakar Abdullahi, Babban Limamin Yelwa, Gindin Akwati a Karamar Hukumar Barkin Ladi, Jihar Plateau, ya rasu.
Marigayi limamin ya shahara a cikin gida da waje a watan Yuni na shekarar 2018, lokacin da ‘yan bindiga suka kai hare-hare kan wasu al’ummomi a Barkin Ladi.
A wancan lokaci, Imam Abdullahi ya buɗe masallacinsa da gidansa domin ba Kiristoci ɗaruruwa mafaka, inda rahotanni suka nuna cewa ya ceci kusan rayuka 300. Ya ƙi miƙa su ga maharan duk da barazanar da aka yi masa na rasa ransa.
Jarumtaka da tausayin da ya nuna sun jawo masa yabo da karramawa daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da lambar yabo ta International Religious Freedom Award da gwamnatin Amurka ta ba shi a shekarar 2019.
Gwamnatin Jihar Plateau, a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a ga Gwamna, Gyang Bere, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, ta bayyana jimami kan rasuwar marigayi limamin.
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwar Imam Abdullahi a matsayin “babban rashi ga iyalansa, al’ummarsa da kuma Jihar Plateau baki ɗaya.”
A cewar sanarwar, gwamnan ya ce rayuwar limamin ta kasance cike da “ƙwazo wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da kare masu rauni, musamman mata da yara.”
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamna Mutfwang ya lura cewa rasuwar ta zo ne a lokacin da jihar ke matuƙar buƙatar shawarwari, hikima da kuma haɗa kan al’umma irin na Imam Abubakar Abdullahi.
“Ya yi kira ga iyalansa da daukacin al’umma da su ɗauki kwanciyar hankali da sanin cewa marigayi limamin ya rayu rayuwar imani, tausayi da adalci, tare da barin gado na hidima da zaman lafiya tsakanin al’ummomi.”
