Shahararren mai shirya bukukuwa kuma fitaccen dan kasuwa, Cubana Chief Priest, ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Cubana Chief Priest ya tsaya takarar neman tikitin APC ne domin wakiltar mazabar Orsu/Orlu/Oru East ta jihar Imo a zaben shekarar 2027.
Sai dai ya fadi zaben ne a hannun Canice More Nwachukwu, wanda shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar a yanzu. Nwachukwu na kan wa’adinsa na biyu a majalisar.
An dai san Cubana Chief Priest da nuna goyon baya sosai ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyyar APC mai mulki.
Haka kuma, an taba nada shi a matsayin daraktan kungiyar City Boy Movement (CBM) ta jihar Imo, wata kungiyar matasa da ke mara wa Tinubu baya domin sake tsayawa takara karo na biyu.
