Trends

Zaben Majalisar Wakilai : Attajiri Ya Yi Watsi da Sakamakon Fidda Gwani

Wani dan takarar jam’iyyar APC mai neman kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya daga mazabar Balanga/Billiri a jihar Gombe, Alfred John Attajiri, ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na kai tsaye da aka gudanar ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Attajiri ya bayyana sakamakon da jami’in tattara sakamako ya sanar a matsayin abin mamaki kuma wanda ba zai amince da shi ba, yana mai cewa ba a gudanar da zabe ba ko kadan.

Ya ce, “A dukkanin kananan hukumomin Balanga da Billiri, akwai kwararan hujjoji ta hanyar bidiyo, hotuna, bayanan shaidu da rahotanni da ke nuna karara cewa babu wani sahihin zabe da aka gudanar kafin a sanar da sakamako.

“Wannan lamari ba kawai cin mutunci ne ga hakkokin dimokuradiyyar mambobin jam’iyya da wakilai ba, har ila yau yana iya lalata amincewa da kima da APC ta gina tsawon shekaru.”

Yayin da yake jaddada biyayyarsa da jajircewarsa ga jam’iyyar, Attajiri ya gargadi cewa idan aka bari rashin adalci yana faruwa a bayyane, ‘yan Najeriya za su rasa fata kan yiwuwar gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027.

Saboda haka, ya roki Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda, da su gaggauta shiga tsakani domin dawo da fata, adalci da kuma karfafa amincewa da jam’iyyar a matsayin cibiyar dimokuradiyya ta gaskiya.

Ya ce, “Yin shiru kan wannan lamari zai kara karfafa rashin gaskiya tare da raunana imanin talakawan mambobin jam’iyya da suka yi imani da adalci, bin ka’ida da bai wa kowa dama iri daya.”

Haka kuma, Attajiri ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu natsuwa, lumana da bin doka, yana mai cewa yana da yakinin cewa gaskiya za ta yi nasara kuma ba za a iya dakatar da muryar jama’a har abada ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *