Trends

Gwamnatin Tinubu Ta Lalata Dimokuradiyya – Galadima

Sakataren Kwamitin Amintattu na jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da lalata dimokuradiyya a Najeriya.

Galadima ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ta kafa wani kwamiti tun kafin a gabatar da kudirin dokar zabe ga Majalisar Tarayya.

Ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin taron masu neman takara na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) da aka gudanar a Abuja.

Hakazalika, ya ce an tsara Dokar Zabe ta 2026 ne domin takura wa jam’iyyun adawa.

A cewarsa, “Lokacin da Majalisar Tarayya ta kammala tattaunawa tare da amincewa da kudirin dokar zaben, cikin awa guda shugaban kasa ya sanya hannu a kai.

“Shin ya samu damar nazarin dokar kuwa? Wannan yana nuna cewa tuni an shirya wata doka a gabansa.

“Daya daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa, wanda ya shafi wannan taro, shi ne cewa hanya biyu kawai aka bari jam’iyyu su samar da ‘yan takara. Ko dai ta hanyar maslaha ko kuma zaben fidda gwani kai tsaye.

“A tunanin APC da gwamnatinta, sun yi zaton jam’iyyun adawa ba za su iya zama su cimma matsaya ta bai daya ba.

“Idan kuma ba za su iya yin hakan ba, hanyar da ta rage musu ita ce su gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye. Ina mai tabbatar muku cewa babu wata jam’iyyar adawa da za ta gudanar da irin wannan zabe ta fito babu matsala.”

Galadima ya kara da cewa jam’iyyar NDC ita ce mafi karfin dandalin siyasa da za ta iya kalubalantar APC tare da kawar da ita daga mulki.

Ya ce jam’iyyar ba za ta iya gudanar da zaben fidda gwani ba saboda akwai yiwuwar a tura wasu mutane domin tayar da tarzoma har ta rasa dan takara.

Saboda haka, ya bukaci mambobin jam’iyyar da su hada kai, su kasance masu biyayya ga jam’iyyar da kuma yanke shawarar dattawa da manyan masu ruwa da tsaki a mazabunsu.

Ya ce duk wanda ya fito a matsayin dan takara a kowace mazaba, wajibi ne kowa ya mara masa baya domin samun nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *