Zaben Majalisar Wakilai : Attajiri Ya Yi Watsi da Sakamakon Fidda Gwani
Wani dan takarar jam’iyyar APC mai neman kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya daga mazabar Balanga/Billiri a jihar Gombe, Alfred John Attajiri, ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na kai tsaye da aka gudanar ranar Asabar. A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Attajiri ya bayyana sakamakon da jami’in tattara sakamako…
