Matatar Dangote ta fara lodin man fetur na awanni 24 a rana domin biyan bukatar Najeriya ta yau da kullum da ta haura lita miliyan 50 na man fetur (Premium Motor Spirit – PMS).
Manajan Darakta na matatar, David Bird, ya bayyana cewa tuni ake yin lodin man da dare domin ƙara yawan samarwa.
“Mun riga mun fara lodin man fetur da daddare… kuma za mu iya ci gaba da samar da fiye da lita miliyan 50 a rana,” in ji Bird.
Ya ce matatar na da burin ci gaba da samar da man fetur da yawa tare da tabbatar da daidaiton wadatar mai a ƙasar, har ma da samun damar ci gaba da aiki yayin da ake gyaran wasu sassa.
“Mun gina wannan sassauci a cikin tsarinmu ta yadda za a iya cire wasu sassa domin gyara, amma duk da haka mu ci gaba da biyan bukatar kayayyakin da aka gama,” Bird ya bayyana.
Ana sa ran wannan mataki zai ƙara ƙarfafa tsaron makamashi a Najeriya, ya taimaka wajen daidaita farashin man fetur, tare da tallafa wa harkokin tattalin arziƙi.
“Samun samar da mai a cikin gida na rage tasirin sauye-sauyen farashi a kasuwannin duniya, ko na danyen mai ko na kayayyakin da aka sarrafa,” in ji Bird.
