Kashi 20 na Mutuwar Mata Masu Juna Biyu a Duniya na Faruwa ne a Nigeriya — CJID

Centre for Journalism Innovation and Development (CJID) ta bayyana cewa Najeriya na daukar kusan kashi 20 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu da ke faruwa a duniya, tana mai bayyana lamarin a matsayin “mummunar matsala ta tsarin kiwon lafiya da ake yi wa shiru.”

Manajar Shirye-shirye ta kungiyar, Felicia Dairo, ta bayyana hakan yayin wani taron horar da ‘yan jaridar lafiya na kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja.

Ta ce rashin gaskiya da rikon amana wajen gudanar da harkokin kiwon lafiya, rashin bayyana kasafin kudade yadda ya kamata, da kuma raunin binciken aikin jarida sun kara ta’azzara matsalar.

“A Najeriya na daukar kusan kashi 20 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a duniya, yayin da adadin mace-macen ke ci gaba da kasancewa mai matukar tayar da hankali,” in ji ta.

Duk da alkawuran da gwamnati ta sha yi, Dairo ta ce har yanzu kudaden da ake warewa bangaren lafiya ba su kai kaso 15 cikin 100 da aka amince da shi a Yarjejeniyar Abuja ba.

Ta ce hakan ya sa cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da dama ba su da ruwa, wutar lantarki ko magunguna masu muhimmanci.

Dairo ta zargi hukumomin gwamnati da boye gazawa ta hanyar amfani da bayanai marasa hadewa da kuma kasafin kudade da jama’a ba sa iya samu cikin sauki.

“Yau da kullum kanun labaranmu na bayyana irin wadannan munanan abubuwa da ke faruwa ga daidaikun mutane, amma mafi yawan lokuta muna dogaro ne da sanarwar gwamnati da ke cewa komai na tafiya yadda ya kamata,” in ji ta.

Ta bukaci ‘yan jarida su rungumi aikin bincike mai amfani da sahihan bayanai domin gano yadda ake karkatar da kudaden kiwon lafiya.

“Ba za mu iya amsa wadannan tambayoyi da rubuce-rubucen ra’ayi kawai ba. Dole ne mu amsa su ta hanyar aikin jarida mai dogaro da kwararan bayanai,” ta kara da cewa.

Horon ya mayar da hankali ne kan muhimman fannoni shida da suka hada da kula da lafiya matakin farko, lafiyar uwa da yara, tsara iyali, rigakafi, abinci mai gina jiki da cututtuka masu yaduwa.

An ce horon zai taimaka wa ‘yan jarida wajen bibiyar kasafin kudade da gano gibin rikon amana a bangaren lafiya.

Dairo ta kammala da cewa ingantaccen aikin jarida na bincike yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da an dorawa hukumomi alhaki da kuma ganin cewa kudaden kiwon lafiya suna haifar da sauyi mai anfani ga iyaye mata da al’ummomin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *