National Health Insurance Authority (NHIA) ta umurci dukkan kamfanonin haya ta manhajojin waya, kai abinci da sufuri ko isar da kaya a Najeriya da su samar wa ma’aikatansu inshoran lafiya na dole.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar 15 ga watan Mayun 2026, NHIA ta ce wannan mataki ya yi daidai da umarnin shugaban kasa na watan Satumban 2025 wanda ya wajabta inshoran lafiya ga dukkan ‘yan Najeriya da mazauna kasar bisa tanadin Dokar NHIA ta shekarar 2022.
Sanarwar da aka aika zuwa ga “Dukkan Kamfanonin Sufuri da Isar da Kaya Ta Manhajoji a Najeriya” ta bayyana cewa:
“Dukkan masu aikin kansu da ma’aikatan da ke aiki a karkashin manhajoji dole ne su samu damar inshoran lafiya.”
Hukumar ta gargadi cewa bin wannan umarni zai kasance cikin sharuddan samun lasisi, izini da amincewar hukumomi, tana mai cewa rashin bin dokar ya saba wa tanade-tanaden kasa.
Daraktan Sashen Ma’aikatan Tsari na NHIA, Ajodi N.N., ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin Darakta Janar na hukumar.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan jin dadin ma’aikatan tattalin arzikin zamani, musamman direbobin haya da masu kai kaya, wadanda galibi ke biyan kudin jinya daga aljihunsu.
Bangaren sufuri da kai kaya ta manhajoji a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba cikin ‘yan shekarun nan sakamakon karuwar birane, rashin aikin yi da kuma bunkasar fasahar zamani ta kamfanoni irin su Uber da Bolt da kuma kamfanonin kai abinci.
Yawancin ma’aikatan wannan bangare ana daukarsu a matsayin masu aikin kansu, lamarin da ya haifar da muhawara kan hakkokin ma’aikata da damar samun kariyar walwala ta gwamnati.
Dokar NHIA ta shekarar 2022, wacce ta maye gurbin dokar tsohuwar Hukumar Inshoran Lafiya ta Kasa, ta wajabta inshoran lafiya ga dukkan ‘yan Najeriya da mazauna kasar bisa doka.
Ana kuma sa ran gwamnatocin jihohi za su kafa nasu tsare-tsaren inshoran lafiya domin fadada damar samun kulawar lafiya ga jama’a.
Sai dai duk da wannan tsarin, miliyoyin mutane har yanzu ba su da inshoran lafiya, yayin da mafi yawan kudaden jinya ke ci gaba da fitowa kai tsaye daga aljihun jama’a, abin da ke nuna muhimmancin aiwatar da inshoran lafiya a bangaren tattalin arzikin zamani.

