Cardoso: Hauhawar Farashi na Wucin Gadi ce Duk da Karin da aka Samu na Watanni Biyu

Yemi Cardoso Shugaban babban Bankin Najeriya wato CBN

Gwamnan Central Bank of Nigeria (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa matsin hauhawar farashi da ake gani a kasar nan a halin yanzu na wucin gadi ne duk da cewa an samu karin hauhawar farashi na tsawon watanni biyu a jere.

Cardoso ya bayyana hakan ne ranar Laraba bayan kammala taron kwamitin manufofin kudi na 305 da aka gudanar a Abuja, inda babban bankin kasar ya bar kudin ruwa na manufofin kudi a kashi 26.5 cikin 100 tare da barin sauran muhimman manufofin kudin ba tare da sauyi ba.

Ya ce duk da cewa hauhawar farashi ta dan karu a watannin baya-bayan nan, musamman sakamakon matsalolin tattalin arziki daga kasashen waje, kwamitin MPC na da yakinin cewa yanayin tattalin arzikin kasar a yanzu yana da karfi da zai taimaka wajen dawo da saukar farashi.

“Ko da yake hauhawar farashi ta karu kadan a watanni biyu a jere sakamakon matsalolin waje, kwamitin MPC ya fahimci cewa lamarin na wucin gadi ne kuma yana da yakinin cewa yanayin tattalin arzikin kasar yana da karfin da zai taimaka wajen rage hauhawar farashi,” in ji Cardoso.

A cewarsa, rikicin Gabas ta Tsakiya ya kara matsin lamba kan farashin makamashi, kudin sufuri da harkokin jigilar kaya a duniya, amma tasirin hakan a Najeriya bai yi tsanani sosai ba saboda sauye-sauyen tattalin arziki da aka yi tun da farko.

Ya bayyana cewa daidaiton farashin canjin kudade, karuwar ajiyar kudaden ketare, karfin manufofin kudi, tsarin bankuna mai karfi da kuma kokarin da gwamnati ke yi wajen daidaita kasafin kudi suna taimakawa tattalin arzikin kasar wajen jure matsalolin waje.

Gwamnan CBN ya ce kwamitin ya gamsu cewa har yanzu akwai yanayin da ake bukata domin tabbatar da daidaiton farashi, yana mai cewa akwai bukatar ci gaba da taka-tsantsan a manufofin kudi domin dakile tsammanin karin hauhawar farashi da kare daidaiton tattalin arziki.

Dangane da alkaluman hauhawar farashi, Cardoso ya bayyana cewa babban adadin hauhawar farashi ya karu zuwa kashi 15.69 cikin 100 a watan Afrilun 2026 daga kashi 15.38 cikin 100 a watan Maris, musamman sakamakon karin farashin abinci da kudin sufuri.

Sai dai ya ce a bangaren core inflation, an samu sauki zuwa kashi 15.86 cikin 100 a watan Afrilu daga kashi 16.21 cikin 100 a watan Maris, yayin da matsakaicin hauhawar farashi na watanni 12 ya ragu karo na shida a jere zuwa kashi 19.16 cikin 100.

Kwamitin MPC ya kuma bar Cash Reserve Ratio a kashi 45 cikin 100 ga bankunan kasuwanci da kashi 16 cikin 100 ga merchant banks, yayin da kudaden gwamnati da ba sa karkashin TSA za su ci gaba da kasancewa karkashin kaso 75 cikin 100 na CRR.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *