Kasafin Kuɗin 2026: Bangaren Sufurin Jiragen Sama Ya Samu Naira Biliyan 87.3

NCAA NCAA

Don Inganta Ababen More Rayuwa
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 87.3 ga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya tare da wasu hukumomi hudu a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka miƙa wa Majalisar Ƙasa a watan Disambar da ya gabata.

Adadin ya ragu idan aka kwatanta da Naira 105,953,496,365 da aka ware wa bangaren a kasafin 2025, amma ya karu idan aka kwatanta da Naira 63,317,450,275 da aka tanada masa a shekarar 2024.

Bugu da ƙari, manyan ayyuka uku da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar za su lakume kusan Naira biliyan 10, kamar yadda daftarin kasafin kuɗin da jaridar The Guardian ta samu ya nuna.

Ayyukan sun haɗa da faɗaɗa tashar jiragen sama ta General Aviation Terminal (GAT) a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano (MAKIA), Kano, da kuɗin Naira biliyan 1; mayar wa Gwamnatin Jihar Kebbi Naira biliyan 4 a matsayin kuɗin gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi; da kuma gina ginin hedikwatar ma’aikatar da gidajen ma’aikata na Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da hukumominta da kuɗin Naira biliyan 5.

Ƙarin bayani kan kasafin Naira biliyan 87 na shekarar 2026 ya nuna cewa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya ta samu Naira 50,646,938,934; Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta samu Naira 11,836,942,378; yayin da Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya (NCAT), Zariya, ta samu Naira 11,281,209,862, da sauransu.

Sai dai Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ba su shiga cikin kasafin 2026 ba. Hukumomin biyu ana ɗaukar su a matsayin masu samar da kuɗaɗen shiga da kansu, duk da cewa gwamnati na ɗaukar nauyin ayyukansu.
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) kuwa, karon farko cikin shekaru biyar, ta shiga cikin kasafin kuɗin.

A halin da ake ciki, ayyukan uku da aka ambata a sama sun kasance a cikin kasafin 2025, inda aka ware musu adadin kuɗi iri ɗaya. Amma ba a bayyana ko an saki kuɗaɗen ga ma’aikatar a shekarar kasafin da ta gabata ba, wanda hakan ya sa suka sake bayyana a kasafin 2026.

Haka kuma, gwamnati ta kashe Naira biliyan 5 wajen sayen muhimman kayan tsaro da kariya a filayen jiragen sama a faɗin ƙasa, ciki har da takardar shaidar filayen jiragen sama, kayan hasken filin jirgi na rukuni na uku (Category III Airfield Lighting) da kayan kwato jirgin sama da ya lalace.

Wani babban aikin da ma’aikatar za ta aiwatar a shekarar 2026, kamar yadda kasafin ya nuna, shi ne gina Jami’ar Aerospace ta Abuja, da kuɗin Naira biliyan 3.

A wani bangare kuma, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira 84,560,242,389 ga Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital (Comtech) da hukumomi biyu a cikin kasafin 2026.

Kasafin ya nuna cewa Hukumar Tauraron Dan Adam ta Sadarwa ta Najeriya (NigComSat) ta samu Naira 9,902,876,431, yayin da Hukumar Wasikun Najeriya (NIPOST) ta samu Naira 28,599,720,151. Ma’aikatar kuma za ta yi aiki da Naira 46,057,645,807 a shekarar.

Kuɗin albashi na ma’aikatar ya kai Naira 1,701,588,769; na gudanarwa (overhead) Naira 760,222,984; yayin da na ayyukan ci gaba (capital) ya kai Naira 43,595,984. Ga NigComSat kuwa, an ware Naira 2,640,278,983 don albashi; Naira 240,946,815 don overhead; da Naira 7,021,650,633 don ayyukan ci gaba.

Gaba ɗaya, ana sa ran ma’aikatar za ta kashe Naira biliyan 32.9 kan albashi, Naira 1,001,169,799 kan overhead, da Naira biliyan 50.7 kan ayyukan ci gaba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kasafin kuɗin, mai taken “Kasafin Haɗa Kai, Sabunta Juriyar Tattalin Arziki da Raba Wadata,” an tsara shi ne domin ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arziki da aka fara da kuma mayar da alamomin daidaiton tattalin arziki zuwa ingantaccen rayuwa ga ’yan Najeriya.

A cikin kasafin, Ma’aikatun Ayyuka (Works), Tsaro (Defence) da Ilimi (Education) sun samu Naira tiriliyan 3.4, Naira tiriliyan 3.2 da Naira tiriliyan 2.3, bi da bi.

Sauran sun haɗa da Lafiya da Harkokin Jama’a (Naira tiriliyan 2.1); Noma da Tsaron Abinci (Naira tiriliyan 1.4); Harkokin ’Yan Sanda (Naira tiriliyan 1.3); Yankin Neja Delta (Naira tiriliyan 1.3); Wutar Lantarki (Naira tiriliyan 1.1); da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wadda ta samu Naira tiriliyan 1.