Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.764 a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin tallafa wa sabbin ɗalibai 300 na Najeriya a ƙarƙashin shirin Tallafin Karatu na Yarjejeniyar Ilimi ta Ƙasashe Biyu (Bilateral Education Agreement – BEA).
An jero wannan tanadi a ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma zai rufe kuɗaɗen alawus-alawus, inshorar lafiya, tafiye-tafiye, da sauran muhimman buƙatu na ɗaliban.
Wannan na daga cikin jimillar kasafin kuɗin ma’aikatar na shekarar 2026, wanda ya kai Naira 2,398,761,320,016.
Wannan mataki ya zo ne duk da cewa a bara gwamnati ta sanar da dakatar da shirin, tana mai cewa yana ɓarnatar da kuɗaɗen jama’a, tare da nuna cewa yawancin darussan da ake karantawa a ƙarƙashin shirin suna samuwa a jami’o’in Najeriya.
Bayanai daga daftarin kasafin kuɗin sun nuna cewa an ware Naira biliyan 1.764 domin aiwatar da sabbin tallafin karatu 300 ga ’yan Najeriya da za su yi karatu a ƙasashen da ke da yarjejeniyar ilimi da Najeriya, ƙarƙashin lambar kasafi ERGP24230073.
Haka kuma, an tanadi Naira miliyan 105 domin tantance makarantu na shirin BEA a ƙasashe 12 ta hannun jami’an Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ƙarƙashin lambar kasafi ERGP24230092.
Bugu da ƙari, an ware Naira biliyan 5.6 ƙarƙashin lambar kasafi ERGP24230060 domin kula da ɗalibai 1,532 da ke ci gaba da karatu a ƙarƙashin shirin BEA a ƙasashen da ke bayar da tallafin. Wannan ya haɗa da biyan alawus na ƙarin tallafi, kula da lafiya, inshorar lafiya, kayan sanyi, da alawus na karatun digiri na gaba.
Ana sa ran waɗannan kuɗaɗen za su rufe buƙatun ɗaliban Najeriya da ke karatu a ƙasashe kamar Rasha, China, Cuba, Romania, Turkiyya, Tunisiya, Aljeriya, Morocco, Serbia, Hungary, Ukraine, Mexico, Venezuela da Kazakhstan.
