Trends

NARD Ta Dakatar da Yajin Aikin da Ta Shirya

Kungiyar Likitocin Asibitin Koyarwa ta Najeriya (NARD) ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya fara wa a ranar Litinin, 12 ga Janairu, bayan shisshigin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Likitan sun yi barazanar shiga yajin aiki ne sakamakon rashin cika wasu muhimman bukatunsu, ciki har da biyan bashin karin girma da albashi, dawo da da kuma kammala yarjejeniyar tattaunawar albashi da sharuddan aiki (CBA) a kan lokaci, fayyace manufofi kan tsallake mataki/ matakin shigar manyan shugabanni, da kuma gazawar aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a baya, da sauransu.

A baya, Kotun Kwadago ta Kasa (National Industrial Court) da ke zamanta a Abuja ta hana kungiyar da wasu jami’anta biyu shiga duk wani yajin aiki daga ranar 12 ga Janairu, 2026.

Mai shari’a E. D. Subilim ne ya bayar da wannan umarnin wucin gadi a cikin karar da aka yi wa rajista da lamba NICN/ABJ/06/2026, wadda Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyan Tarayya suka shigar a kan NARD.

Da yake magana da jaridar Daily Trust, Shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana cewa an cimma matsayar dakatar da yajin aikin ne bayan Mataimakin Shugaban Kasa ya shiga tsakani tare da magance wasu daga cikin bukatun kungiyar.

“Mun dakatar da yajin aikin da muka shirya fara wa gobe saboda shisshigin Mataimakin Shugaban Kasa. Ya kira mu, ya shiga lamarin, kuma an warware wasu daga cikin matsalolinmu,” in ji Suleiman.

Ya kara da cewa Mataimakin Shugaban Kasa ya nemi karin lokaci domin magance sauran matsalolin, bukatar da Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) ta amince da ita.

“Ya nemi karin lokaci don warware sauran batutuwan, kuma NEC ta amince masa da wannan lokaci,” in ji shi.
Suleiman ya ce za a fitar da karin bayani ga mambobin kungiyar da kuma jama’a nan gaba kadan.

“Za a fitar da cikakken bayani daga baya. Amma ba za a yi yajin aiki ranar Litinin ba,” in ji shi.