Hukumar masu ba da wutar lantarki na gashin kansu, Nigerian Independent System Operator (NISO) ta sanar da kwastomominta a jihohin Adamawa, Gombe, Bauchi, Borno da Yobe cewa za a yi katsewar wutar lantarki a kan layin wutar Jos–Gombe mai ƙarfin 330kV daga ranar 9 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu.
A cikin wata sanarwa, NISO ta ce za a rika katse wutar ne duk ranar Alhamis zuwa Lahadi daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Hukumar ta bayyana cewa katsewar ta zama dole domin girka sabuwar fasahar sadarwa ta Optical Ground Wire (OPGW) a kan layin wutar.
Ta ƙara da cewa wannan aikin na daga cikin ƙoƙarin inganta aikin grid ta hanyar ƙarfafa tsarin sa ido da sarrafa wuta (SCADA), tsarin kula da makamashi (EMS), da hanyoyin sadarwa.
A cewar sanarwar, ana sa ran aikin zai ƙara inganta sa ido kai tsaye, gano matsaloli da wuri, daidaita lodin wuta, da kuma inganta isar da wutar lantarki a yankin.
Sai dai hukumar ta ce a lokacin katsewar, za a ci gaba da samar da wuta ta hanyar wasu layukan 132kV da ake da su.
Duk da haka, ta yi gargaɗin cewa saboda ƙarancin ƙarfi da matsalolin da ke tattare da waɗannan layukan, kwastomomi na iya fuskantar raguwar wuta da takaitaccen sabis a lokacin katsewar.
NISO ta kuma bayyana cewa tana aiki tare da masu ruwa da tsaki ciki har da kamfanonin rarraba wuta na Jos da Yola, da kuma Transmission Company of Nigeria (TCN), domin tabbatar da cewa an sarrafa katsewar yadda ya kamata.
A ƙarshe, hukumar ta ce bayan kammala aikin, ana sa ran samun ingantacciyar wuta mai dorewa, kyakkyawar haɗin kai a grid, da kuma ingantaccen tsarin rarraba wuta a yankin.
